Mata sun koka da rashin armashin Ranar Masoya saboda ƙarancin Naira

Daga AMINA YUSUF ALI

Bincike ya nuna cewa, ƙarancin tsabar Naira ya yi matuƙar rage armashi ga bikin ranar masoya na bana.

A ranar Larabar da ta gabata, 14 ga Fabrairu, 2023, ne dai wasu mata ma’aikata mazauna Birnin Tarayyar Abuja suka koka da yadda ƙarancin takardun Naira ya hana su samun kyautar Ranar Masoya daga mazajensu da kuma samun damar fita shagalin raya soyayya. 

Wani ɓangare kuma na matan da suka zanta da manema labarai sun bayyana yadda ƙarancin takardun Nairar ya hana su samun damar fita yawon shaƙatawa da mazajensu a ranar masoya. 

Ita dai ranar masoya wani biki ne da ake gudanarwa ranar 14 ga watan Fabarairun kowacce shekara don masoya su raya kuma su sabunta soyayyarsu. 

Wata ma’aikaciya mai suna Chelsea Ndubaku, ta bayyana wa manema labarai irin yadda ta yi kwanan baqin ciki bayan da kuɗi suka gagara fita a ATM, abinda ya yi sanadiyyar dole suka soke fiyar da za su yi da maigidanta.

A cewar ta, shekaru biyar kenan da suka yi aure da mijinta kuma bai tava yin fashin kai ta yawon shaƙatawa ba duk ranar da ranar bikin masoyan ta zagayo.  

Hakazalika, mata da dama da majiyar tamu ta zanta da su sun bayyana takaicinsu ga wannan alamari da ya hana su yin shagalinsu na ranar masoya. 

Hakan ta faru ne saboda yadda kuɗaɗe suka yi wahala a na’urorin ATM kuma babu a POS. wasu lokutan idan aka ce za a yi turi kuma a kwashe maka kuɗin asusu a ƙi kuma ba ka. Sannan kuma ‘yan kasuwa da dama sai su ce ba sa karɓar turi sai kuɗi-hannu.