Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
An gudanar da Sallar jana’izar ‘yan-sakai mutum 10 da ‘yan bindiga su ka kashe a ƙaramar hukumar Anka ta Jihar Zamfara a jiya Asabar kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal a saƙon jajantawa a shafinsa na Facebook ya bayyana cewar “na samu labarin kwantan ɓauna da ‘yan bindiga suka yi wa wasu daga cikin askarawa a ƙaramar hukumar Anka”.
A cewar Gwamna Dauda, lamarin ya faru ne jiya, biyo bayan farmakin da gamayyar jami’an tsaro (ciki har da askarawa) ƙarƙashin jagorancin sojojin Nijeriya suka kai wa sansanin ‘yan bindiga a dajin Sunƙe, wanda aka samu gagarumar nasarar kashe da dama tare da ƙwato makamai masu tarin yawa.
“Rahoton da na samu shi ne, a hanyarsu ta dawowa ne ‘yan bindiga suka yi musu kwanton ɓauna a Bagega inda suka kashe askarawa shida, da ‘yan sa-kai huɗu, waɗanda aka yi jana’izarsu da safiyar nan”.
Gwamnan ya bayyana cewa akwai mutum uku da ba a gani ba, biyu askarawa, ɗaya ɗan sa-kai.
Gwamnan hakazalika ya Ƙara da cewar, tun faruwar lamarin ya bada umurnin a ɗauki matakin bayar da agajin gaggawa ga waɗanda suka samu raunuka, sannan a bayar da tallafin gaggawa ga iyalan waɗanda suka rasu.
“A madadin gwamnatin Jihar Zamfara, ina addu’ar Allah ya amshi shahadan waɗannan bayi nashi da suka sadaukar da rayuwarsu don kariya ga al’ummarsu, Allah ya jiƙansu, ya ba ‘yan uwa da iyalai haƙurin rashi”.
” Allah ya kawo mana ƙarshen matsalar tsaro a Jihar Zamfara, Arewa da ma Nijeriya gaba ɗaya”. Gwamna Dauda ya ce
