An buƙaci gwamnan Kano da ya sauka daga kan kujerarsa-Rikicin Masarauta

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Wata tawagar al’ummar Jihar Kano ta yi kira ga gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf da ya sauka daga kan kujerar shugabancin Jihar domin martaba doka da oda.

Wani mamban tawagar mai suna Muhammad Bello ya faɗi hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce sun yi kiran ga gwamnan ne sakamakon ƙin biyayya ga hukuncin da kotu ta yi na rushe cancantar zaman Sunusi Lamido Sunusi a matsayin halstaccen Sarki.

Bello ya ƙara da cewa, ƙin amincewa da hukuncin Alƙali Abdullahi Liman a babbar kotun tarayya ga gwamnan, alama ce dake nuna cewa yana rashin ladabi ga doka da oda, don haka suke ganin dacewar ya sauƙa daga muƙamin nasa.

Sanarwar ta ƙara da cewa, matuƙar gwamnan ya ƙi sauka, to zasu ɗaura masa laifin duk wani tashin-tashina da ya/zai faru a tsakanin al’umma kan rikicin Masarautar, don haka ya ce zasu yi zanga-zangan nuna ƙin goyon bayansu ga cigaba da mulkinsa a duk wuraren da suka dace, ciki har da fadar gwamnatin Jihar da yakin gidan Jihar dake Abuja da makamantansu.

By Babaji