An buƙaci gwamnatin Katsina ta gyara hanyar Ɗan Ali zuwa Musawa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

An buƙaci majalisar zartaswa ta gyara hanyar Marabar Ɗan Ali, Ɗan Ali, Dangani, Kwanar Gwarjo zuwa cikin garin Musawa, dukkansu dake cikin ƙaramar hukumar Ɗanmusa da Musawa.

Yan majalisar dokoki da ke wakiltar ƙananan hukumomin Ɗanmusa da Musawa Hon. Aminu Garba Sai Baba, Musawa Hon. Lawal H. Yaro Away, Su ka gabatar da kudirin buƙatar gyara hanyar, a zaman majalisar ƙarƙashin jagorancin Kakakin majalisar Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura.

Da yake gabatar da jawabinsa, yayin da yake gabatar da ƙudirin, ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Musawa Hon. Lawal H. Yaro Away ya bayyana cewa” gyara hanyar zai taimaka ma harkokin rayuwar yau da kullum na al’ummar yankin.

Kazalika, shima ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Dutsinma Hon. Muhammad Abubakar Khamis ya gabatar da ƙudirin bukatar gina hanya daga kauyen Kofa, Yar Ruma dake cikin mazaɓar Kutawa, da kuma daga Dogon Zoo zuwa Doka dake cikin mazabar Karofi (B) dake cikin ƙaramar hukumar Dutsinma.

Bayan tattaunawa akan ƙudirorin, daga ƙarshe majalisar ta amince da ƙudirorin, inda Kakakin majalisar ya umurci akawun majalisar da ya tura ma ɓangaren zartarwa domin ɗaukar matakin da ya dace.

By ukarofi