An buƙaci ’yan kasuwar Bichi su rungumi tsarin kasuwanci na zamani

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

An jaddada buƙatar ‘yan kasuwar Bichi su rungumi dabarun kasuwancin zamani domin faɗaɗa harkokinsu da tabbatar da ci gaba mai ɗorewa a yankin.

Shugaban Hukumar Raya Kogin Hadejia da Jama’are, Alhaji Rabi’u Sulaiman Bichi, ne ya bayyana haka yayin da ƙungiyar Bichi Traders Multi-Purpose Cooperative Society Limited ta kai masa ziyara a ofishinsa da ke Kano.

A jawabin sa, Alhaji Rabi’u ya nuna jin daɗinsa kan wannan ziyara wadda ya ce tana ƙarfafa zumunci da haɗin kai tsakanin hukumarsa da ‘yan kasuwa.

Ya buƙace su da su ƙara fahimtarsu a fannin lissafi da ƙididdiga, da kuma sabbin hanyoyin kasuwanci da duniya ke bi a yau.

Haka kuma ya shawarce su su riƙa janyo matasa cikin harkokin kasuwanci domin dorewar cigaban da kuma cusa sabbin dabaru a kasuwa.

Shugaban ya ƙara jaddada cewa ƙofarsa a buɗe take ga duk wani lamari da ya shafi cigaban kasuwanci a yankin, tare da yi musu fatan alheri da karin nasara a ƙoƙarinsu na bunƙasa harkar kasuwanci a Bichi baki ɗaya.

A nata ɓangaren, shugaban ƙungiyar ‘yan kasuwar, Alhaji Abubakar Mazahimu Sale, ya nuna matukar farin ciki bisa yadda aka tarbe su, inda ya ce ziyarar ta samo asali ne daga girmamawa da neman shawarwari, musamman ganin cewa Alhaji Rabi’u tsohon dankasuwa ne wanda ya fara kasuwanci tun daga tushe har zuwa matsayin mashahurin dan kasuwa a kasar nan.

Shugaban Kwamitin Dattawan Kasuwa, Alhaji Lawan Ibrahim, shi ma ya jinjinawa Alhaji Rabi’u kan irin aikace-aikacen cigaba da ya kawo a ƙaramar Hukumar Bichi, ciki har da gina Dam din Bela, Malikawa–Garu da kuma garin Kungu, wanda ya ce alamu ne na kishin al’umma da kyakkyawar kishin ƙasa.

By ukarofi