An buɗe cibiyar yaƙi da cutar Poliyo da aka faɗaɗa a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban hukumar kula da lafiya a matakin farko a jihar Katsina, Dr. Shamsuddeen Yahaya, ya jagoranci ƙaddamar da faɗaɗa cibiyar gudanar da ayyukan gaggawa kan cutar Poliyo (Expanded Polio Emergency Operations Centre (EOC) a jihar Katsina, a daidai lokacin da Bola Ahmed Tinubu yaƙe kaddamar da su a Abuja, Sokoto, Kano, da Katsina amma ta yanar gizo, domin inganta kiwon lafiya da kare lafiyar yara da kuma ƙarfafa yaƙi da cutar Poliyo a Najeriya.

Shugaban hukumar ya yaba ma shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a kan gudummuwar da yake badawa kan kula da lafiya a matakin farko a sassan ƙasar.

Ya ce cibiyar ta EOC ta shafe shekaru tana jagorantar shirye-shiryen allurar rigakafi gida-gida, tare da bibiyar duk wani rahoton kamuwa da cutar domin tabbatar da cewa babu wani yaro da aka bari da ita.

Dr. Yahaya ya bayyana cewa, faɗaɗa cibiyar zai samar da ƙarin azama, da ingantaccen tsarin tattara bayanai da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki a hukumar.

A cewarsa, sabon tsarin zai ba da damar bibiyar bayanai kai tsaye daga kowacce gunduma, da tura jami’an lafiya cikin sauri zuwa yankunan da ke da wahalar zuwa, da kuma ɗaukar matakan gaggawa kan cutar CVDPV cikin lokaci.

Haka kuma, ya yabawa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa jagoranci da goyon bayan da yake bayarwa wajen bunƙasa harkar lafiya a ƙasar nan.

Kazalika, ya jinjinawa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, bi sa zuba jari da yake yi a fannin kula da lafiya da tsaron lafiyar al’umma, wanda ya taimaka wajen ganin an samu wannan ci gaba.

Dakta Yahaya ya kuma godewa hukumar NPHCDA da sauran abokan hulɗa na ci gaba bisa irin sadaukarwar da suka yi wajen rage yawaitar cutar Polio a Najeriya da sauran wasu cututtuka na daban.

Ya ƙara da cewa har yanzu akwai aiki a gaban su, musamman wajen tabbatar da cewa an kare kowane yaro daga cututtuka masu haɗari.

Shugaban hukumar, ya yi addu’ar Allah ya sanya wannan cibiya ta zama sanadiyyar kawar da Cutar Polio a jihar Katsina da kasa baki daya, tare da ingantacciyar lafiya ga al’umma baki ɗaya.

By ukarofi