Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban cocin Word of Life Bible Church kuma tsohon shugaban kungiyar CAN, Fasto Ayo Oritsejafor, ya bayyana cewa ya kashe kimanin dala 120,000 wajen jinyar cutar kansa da ya yi fama da ita a kasar Amurka.
A cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Oritsejafor ya ce ya shafe watanni yana karbar magani bayan an gano yana dauke da cutar yayin da yake kasar waje.
Ya bayyana cewa likitoci sun fara gano matsalar ne tare da bukatar a ci gaba da sa ido sosai a kansa, lamarin da ya sa yake yawan zirga-zirga tsakanin Nijeriya da Amurka domin duba lafiyarsa da ci gaba da jinya.
Faston ya ce daga baya lamarin ya tsananta har aka yi masa tiyata, sannan ya shafe lokaci mai tsawo yana murmurewa karkashin kulawar likitoci.
Ya kara da cewa bayan tiyatar ya samu matsalar kamuwa da cuta, wanda hakan ya tilasta likitoci yin amfani da magungunan kashe kwayoyin cuta daban-daban kafin daga bisani lafiyarsa ta daidaita.
A cewarsa, kudin jinyar sun kai kusan dala 120,000, wanda ya hada da kudin tiyata, kwanciya a asibiti da sauran kulawar lafiya da aka ba shi tsawon watanni.
Oritsejafor ya bayyana cewa baya ga tsadar kudin jinyar, ya kuma fuskanci wahalhalu na jiki da tunani saboda tsananin radadi da rashin tabbas da ya rika fuskanta yayin jinyar.
Ya ce mataimakinsa na musamman ya kasance tare da shi a wasu lokuta na jinyar duk da cewa an fara ba shi shawarar kada ya yi tafiya.
Faston ya ce wannan jarabawa ta kara masa karfin imani da hakuri, yana mai cewa ya koyi darasi na juriya da godiya ga Allah.
A karshe, ya karfafa wa masu fuskantar matsaloli gwiwa da kada su yanke kauna, yana mai cewa sauki da nasara na iya zuwa bayan doguwar wahala.
