Jihohi 21 na cikin haɗarin fallatsar cutar Ebola – Gwamnatin Tarayya

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Gwamnatin tarayya ta bayyana jihohi 21 da kuma babban birnin tarayya Abuja a matsayin wuraren da ke cikin haɗarin kamuwa da cutar Ebola, bayan ɓarkewar cutar a ƙasashen Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo da Uganda. Hukumar NCDC ta ce an ɗauki matakin ne domin ƙara shiri da sanya ido kan yiwuwar shigowar cutar Najeriya.

Daraktan hukumar NCDC, Jide Idris, ya bayyana cewa har yanzu ba a samu ɓullar cutar Ebola a Najeriya ba, amma yawaitar cutar a ƙasashen gabashi da tsakiyar Afirka na ƙara haddasa fargabar yaɗuwarta zuwa wasu ƙasashe. Ya ce alamomin Ebola suna kama da na zazzaɓin cizon sauro da Lassa fever, lamarin da ke sa gano cutar cikin gaggawa ya zama ƙalubale.

Jihohin da aka sanya cikin babban haɗari sun haɗa da Legas, Abuja, Ribas, Kano, Enugu, Borno, Akwa Ibom, Kuros Riba, Taraba da Adamawa saboda filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa, iyakoki masu rauni da kuma yawan zirga-zirgar mutane. Sauran jihohin da aka bayyana a matsayin matsakaicin haɗari sun hada da Ogun, Nasarawa, Kaduna, Filato, Kogi, Niger, Jigawa, Katsina, Bauchi, Ebonyi, Abia da Bayelsa.

Hukumar NCDC ta buƙaci gwamnatocin jihohi da su gaggauta ɗaukar matakan kariya, da ƙarfafa bincike a filayen jiragen sama da kan iyakoki, tare da shirya cibiyoyin killace masu ɗauke da cutar. Haka kuma an bai wa jihohi wa’adin sa’o’i 72 domin gabatar da rahoton shirinsu na tunkarar ɓarkewar cutar, yayin da aka tunatar da yadda Najeriya ta yi nasarar daƙile Ebola a shekarar 2014 bayan shigowar wani mai ɗauke da cutar Legas.

By ukarofi