Tawagar Majalisar Dokokin Nijeriya ta yaba wa NAHCON kan Hajjin 2026

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Juma’a tawagar Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta kai wa alhazan Nijeriya ziyara a Mina, a wani yanayi na sauke nauyinta na sanya ido akan harkokin aikin hajjin 2026.

An ɗauki matakin ne domin tabbatar da alhazan Nijeriya sun samu kulawa yadda ya dace a baki ɗaya zamansu a Saudiyya a ƙarƙashin ikon majalisar dokokin.

Rahotanni sun bayyana cewa, a yayin ziyarar, tawagar ta kai ziyarar gani da ido wajen masaukin wucin-gadi na alhazan, inda ta gana da su tare da jami’ai masu alhakin kula da walwalarsu.

A yayin haka ne kodinetoci da alhazai suka bayyana gamsuwa da hidimar da Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON) ta yi musu musamman akan abin da ya shafi masauki da shirye-shiryen ciyarwa.

Haka kuma, alhazan Nijeriyar sun jinina wa nagarta da tsarin abincin da aka riƙa samar musu a zamansu na Mina, saidai sun nemi a ƙara adadin nau’ukan abincin Nijeriya a harkokin hajji na nan gaba musamman saboda mutanen da suka manyanta.

Sun kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa ƙoƙarinsa wajen tabbatar da samun walwala ga alhazan Nijeriya da gudunmawarsa ta ganin an yi nasarar aikin hajjin.

Da yake jawabi yayin ganawar, Sanata Ali Ndume, ya roƙi alhazan da su cigaba da yin addu’o’in nema zaman lafiya, tsaro, ɗorewa da samun nasarori a Nijeriya.

Ya kuma buƙace su da kada su manta da jagororin Nijeriya, iyalansu da sauran ‘yan ƙasa acikin addu’o’insu.

A ƙarshe, ya yi musu alƙawarin cewa za a tabbatar da warware dukkan wata matsala da aka fuskanta a yayin hajjin.

By Babaji