
Jam’iyyar adawa PDP ta zargi Ministan Abuja Nyesom Wike, da ƙoƙarin hana gudanar da taron amincewa da tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan a matsayin ɗan takarar shugaban kasa na wata tsagin jam’iyyar a zaɓen 2027 da ke tafe.
A sanarwar da kwamitin riƙon kwarya na jam’iyyar ya fitar, PDP ta ce masu gidan taro na A Class Event Centre da ke Wuse 2 a Abuja sun sanar musu cewa ana matsa musu lamba domin kada su bai wa jam’iyyar damar gudanar da taron nata.
Tsagin ya ce PDP ta riga ta biya kuɗin wurin tare da cika duk wasu sharudda da ake bukata kafin gudanar da babban taron da aka shirya yi ranar Asabar 30 ga Mayu, 2026.
Haka kuma, PDPn ta ce har ma ta sanar da jami’an tsaro game da taron, tana mai jaddada cewa babu wani abu da zai hana gudanar da shi.
A cewar kakakin jam’iyyar, Ini Ememobong, duk wani yunƙuri na hana taron tamkar ƙoƙarin murkushe adawa ne a tsarin dimukraɗiyya, don haka Wike ba shi da ikon tantance wace jam’iyya ko taro za a bari a gudanar a birnin.
Wannan na zuwa ne bayan hukumar Hukumar Gudanar da Birni FCTA, ƙarƙashin Wike ta gargaɗi masu otal-otal da wuraren taro da su tabbatar suna mu’amala ne kawai da shugabannin jam’iyyun siyasa da INEC ta amince da su.
