
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya mayar da martani ga kalaman jagoran Kwankwasiyya, Rabi’u Musa Kwankwaso, inda ya ce Kwankwason ya taɓa kasancewa ɗan siyasar da ya riƙa samun tallafin shawarwari da taimako a farkon shigar sa harkar siyasa.
Ganduje ya bayyana hakan ne ta bakin shugaban ma’aikatansa yayin da yake kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin bana.
A cewar Ganduje, siyasa tana ginuwa ne akan taimako, jagoranci da haɗin kai, saboda haka babu wani ɗan siyasa da ke samun nasara ba tare da gudunmawar wasu ba.
Ganduje, wanda kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na Ƙasa ne, ya tunatar da yadda ya taimaka wa Kwankwaso a farkon rayuwarsa ta siyasa musamman lokacin zaɓen majalisar dokoki wanda ya kai shi matsayin mataimakin kakaki a Majalisar Wakilai.
Tsohon gwamnan ya kuma ce bai kamata a mayar da batun “uban gida da yaro” cikin siyasar yau ba, domin jama’a na sa ran shugabanni su fi mayar da hankali kan ci-gaba da zaman lafiyar yankunansu.
Kazalika, Ganduje ya buƙaci ‘yan siyasa da magoya bayansu a Kano da su guji kalaman da za su haddasa rarrabuwar kai a tsakanin al’umma da kasancewa masu haɗin kai don ciyar da yankunansu gaba.
