Shugaban NAHCON ya halarci taron bikin Babbar Sallah da Yariman Saudiyya ya shirya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, Ambasada Isma’il Abba Yusuf, ya shiga sahun waɗanda aka gayyata domin halartar taron walimar bikin Babbar Sallah da Mai Alfarma Yarima kuma Fraministan ƙasar Saudiyya Mohammed bin Salman bin Abdulaziz ya shirya domin karrama baƙin Saudi yayin aikin Hajjin 1447.

An gudanar da taron ne a yau Juma’a, 29 ga watan Mayu, 2026 a fadar sarki a Mina, kusa da Makkah a ƙarƙashin jagoran Massallatai biyu masu alfarma, Sarki Salman bin Abdulaziz, inda aka samu halartar manyan malaman duniya, ‘yan difulomasiyya da kuma jagororin hukumomin jigilar alhazai.

Da yake jawabi a taron, Ambasada Yusuf ya yaba wa gwamnatin Saudi bisa ƙoƙarinta na tabbatar gudanar da aikin hajji cikin walwala a kowace shekara ga miliyoyin al’ummar Manzon Allah (SAW).

Ya bayyana cewa, taron ya bayar da damar ƙarfafa alaƙa tsakanin ƙasashen musulmi da hukumomin jigilar alhazai musamman akan lamuran gudanar da fannin.

Shugaban na NAHCON ya kuma jaddada aniyar hukumar wajen tsare gaskiya da adalci, inganta ayyuka da walwalar mahajjata a harkokinta.

Haka kuma, ya tabbatar da cewa NAHCON tana sanya ido akan tawagogyin da aka ɗora wa alhakin ayyuka domin tabbatar da walwalar mahajjatan Nijeriya.

Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Alƙalin alƙalan Nijeriya, Mai Shari’a Kudirat Motonmori Olatokunbo Kekere-Ekun (GCON) da Ministan Labarai da Wayar da kan Al’umma, Alhaji Mohammed Idris da sauransu.

By Babaji