Daga USMAN KAROFI
Tsagin jam’iyyar PDP mai biyayya ga ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya buƙaci tsohon shugaban ƙasa, Dr. Goodluck Jonathan, da ya fito fili ya nesanta kansa daga raɗe-raɗin da ke alaƙanta shi da takarar shugaban ƙasa ta jam’iyyar a zaɓen shekarar 2027. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran tsagin, Jungudo Haruna Mohammed, ya sanya wa hannu.
Tsagin ya bayyana cewa rahotannin da ke cewa jam’iyyar PDP na shirin gudanar da taro domin tabbatar da Jonathan a matsayin ɗan takararta ƙarya ne kuma ba su da sahihanci. A cewarsu, tuni jam’iyyar ta kammala dukkan zaɓukan fidda gwani har da na shugaban ƙasa, inda aka tantance kuma aka bayyana Sanata Sandy Onor a matsayin ɗan takarar PDP na 2027.
Sanarwar ta zo ne bayan tsagin kwamitin riƙon ƙwarya na jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki ya sanar da shirinsa na gudanar da babban taro a Abuja domin amincewa da Jonathan a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa. Sai dai ɓangaren Wike ya ce babu wata hukuma ko sahihin ɓangare na PDP da ya amince da irin wannan taro.
Tsagin ya kuma buƙaci hukumomin tsaro su binciki waɗanda ke yaɗa irin waɗannan rahotanni domin hana tayar da rikicin siyasa a ƙasar. Sun jaddada cewa PDP za ta ci gaba da kare mutuncinta, bin doka da oda, da kuma tabbatar da dimokuraɗiyya a dukkan harkokinta na siyasa.
