
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An samu wata babbar majiya da kada da ƙaramin zaki a gidan tsohon Akanta-Janar na Ƙasa, Ahmed Idris da ke Kano.
Tsohon akantan ya yi aiki ne a muƙamin a zamanin marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda a kwanan nan ya shiga sahun waɗanda ake tuhuma kan wasu kuɗaɗe da adadinsu ya kai sama da Naira biliyan 109 da ake zargin sauya akalarsu.
An ga yadda sunansa ya karaɗe shafukan jaridu a lokacin da Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati, EFCC ta kama shi bisa hannu a badaƙalar kuɗaɗen.
Duk da cewa ana cigaba da bincike akan al’amarin badaƙalar, tsohon akantan ya cigaba da gudanar da matsakaici rayuwa tun bayan barin sa ofis.
Rahotanni sun bayyana cewa, an gano haka ne a lokacin da macijiyar ta tsere daga gidan tare da kutsawa cikin unguwannin Mandawari da Kabara, lamarin da ya haddasa tsoro acikin al’ummar yankunan da makusantansu.
Darakta Manaja na gidan namun daji a jihar, Sadik Kura Muhammad ya tabbatar da cewa an kamo macijiyar da suaran namun dajin da suka haɗa da kada, zaki da ƙaramin zaki, inda aka mayar da su gidan ajiyar namun dajin.
