Yadda aka damfare ni kuɗin maganin jinya da gwamnan Kano ya ba ni – Halisa Muhammad

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Matar, mai suna Halisa Muhammed, wadda tsohuwar jarumar masana’antar Kannywood ce wadda ke fama da ciwon kansar mama (breast cancer), ta koka ne bayan da aka samu wani da ake zargin ɗan damfara ne, Bashir Abdullahi, ya karɓe mata kuɗaɗen da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ba ta domin zuwa neman magani.

Akan haka ne ta rubuta wani saƙo na musamman ga ɗaukacin al’umma domin neman mafita ga halin da ta shiga.

Ga saƙon kamar yadda ta wallafa a shafukan sada zumunta:

“Ina rubuta wannan wasiƙar ne da zuciya mai rauni da tausayi, ina neman adalci daga al’umma, ’yan sanda, da gwamnatin jihar Kano, da dukkan masu rike da madafun iko.

Ni baiwar Allah ce mai fama da ciwon kansa mama da ke bukatar duba lafiyata a kasashen waje.
Kuma na dace mai girma gwamnan jihar Kano ya dauki nauyin yi mun allurai da magunguna.

A cikin wannan hali na, wani bawan Allah mai suna Bashir Abdullahi ya karɓi kuɗina har Naira miliyan bakwai da ɗari biyar (₦7,500,000) da sunan zai taimaka
mini da wani asibiti da ke madina a kasar saudi arabia wajen yin visa zuwa asibitin domin jinya.

Amma abin takaici, bayan ya karɓi kuɗin:

*Visa ta bogi kafin mu tafi
Ya bani tikitin shima na bogi
Nayi sallama da gida na tafi filin jirgi akace mun babu sunana a jerin masu tafiya babu.
Wannan abu ya jefa ni cikin babban raɗaɗi da damuwa, ba wai na rasa kuɗi kawai ba, har ma da lafiyata da rayuwata ke cikin haɗari.

Ina roƙon yan sanda, gwamnati, da al’umma da masu adalci da su taimaka a bi mani hakkina, a binciki lamarin, a kuma tilasta masa mayar da kuɗina.

A rayuwata tana cikin hatsari!

Innalillahi wa inna ilaihirraji’un!

Don Allah ku taimaka mani yadda kuka saba taimakawa saƙon ya isa inda ya kamata yaje

AMBASSADOR &CEO WFCDTF HALISA MUHAMMED.”

A kwanakin baya, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba ta kimanin Naira miliyan 15, don ɗaukar nauyin jinyarta a ƙasar waje. Yanzu haka wasu lauyoyi masu zaman kansu da suke ayyukan kare haƙƙn bil’adama sun shiga lamarin. Al’umma kuma sun zura idanu, don ganin matakan da jami’an tsaro da Gwamnatin Jihar Kano za su ɗauka.

By Babaji