Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Al’ummar garin Libata da ke ƙaramar hukumar Ngaski a Jihar Kebbi sun koka da kamfunan da ke haƙar ma’adanai a yankin su.
Malam Sani Aliyu ɗaya daga cikin matasan yankin ya bayyanawa wakilinmu da cewa waɗannan mutanen sun daɗe suna cin karen su ba babbaka a yankin wajen haƙar ma’adanai da su ke yi ba ƙaƙƙautawa sai dai su mazauna garuruwan da ke zagaye da inda a ke haƙar ma’adanai din ba wani abu da suka amfana da shi sai dai ƙura da manyan motocin su ke barbaɗa musu ba dare ba rana.
Ya ƙara da cewa ya kamata aƙalla a ce sun ɗauki matasan garuruwan da ke zagaye da wuraren amma a maimakon haka sai dai su zo da ma’aikatan su daga waɗansu wurare.
Haka-zalika ba wani abun amfani kamar asibiti, makarantu, tituna ko wani abu na more rayuwa da suka yi saɓanin yadda ya ke a ƙa’ida.
Wakilinmu ya yi tattaki zuwa MUFKAD ɗaya daga cikin mahaƙar ma’adanai a yankin inda ya tarar ana ta haƙar ma’adanai ba ƙaƙƙautawa kuma ya nemi jin ta bakin ɗaya daga cikin shugabannin kamfanin inda ɗaya daga cikin yaran su mai suna Adams ya bayyana cewa ba ya da hurumin magana da yan jarida amma dai ba su da wata matsala da kowa.
Ana dai hasashen da yawa daga cikin masu haƙar ma’adanai din suna yin aikin ne ba bisa ƙa’ida ba saboda ba su da lasisi illa dai wani shiri ne tsakanin su da mahukumta wanda yanzu haka an rufe kamfunnan haƙar ma’adanai da dama a wannan yankin sanadiyyar waɗansu dalilai daban-daban.
Wakilinmu ya nemi jin ta bakin shugaban ƙaramar hukumar mulki ta Ngaski Honarabul Maniru amma dai hakan ba ta samu ba saboda ba ya gari kuma lambar sa ba ta shiga ya tura saƙo amma dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto ba amsa.
