An ga shugaban EFCC yayin da Tinubu ya gayyaci tsohon kantoman Ribas, Ibok-Ete Ibas

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yammacin jiya Laraba Shugaba Bola Tinubu ya gayyaci Kantoman Jihar Ribas, VA Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), zuwa Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa, Ibas, wanda ya bar ofis a ranar 17 ga watan Satumba, 2025 bayan kawo ƙarshen dokar ta-ɓaci a jihar, ya isa Fadar ne da misalin ƙarfe 6:50, inda wasu jami’ai suka tarbe shi tare da masa iso zuwa wajen shugaban ƙasar.

A tare da shi an ga Ministan Kuɗi, Wale Edun da Shugaban Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) Ola Olukoyede, waɗanda ke bada hasashen maudu’in da zaman ya ƙunsa.

Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan da Kakakin Majalisar Dokoki ta Ribas, Martin Amaewhule ya sanar da shirin gudanar da bincike akan kuɗaɗen da aka kashe na tsawon watanni shida da Kantoman ya mulki jihar mai tarin albarkatun mai.

A matsayar da majalisar ta cimma akwai batun bincike akan kuɗaɗen harajin da aka tattara, kwangilolin da aka bayar da wasu al’amuran kuɗi ƙarƙashin jagorancin Ibas.

Jihar Ribas ta samu jimillar Naira biliyan 254.37 daga Asusun Ƙasa (FAAC) a tsakanin watan Maris da Agusta, 2025, wato wa’adin Ibas.

Halartar jagororin Ma’aikatar Kuɗi da EFCC wajen zaman ya sa ake ganin Fadar Shugaban Ƙasa na shirin gudanar da nazari akan lamuran kuɗaɗen jihar da yiwuwar yin da bincike game da asusun jihar ƙarƙashin Ibas.

By Babaji