Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Katsina da haɗin gwiwar gidauniyar Qatar, ta ƙaddamar da bada tallafi ga marayu da marasa galihu 160 a jihar.
Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya ƙaddamar da rabon kayayyakin sana’o’in dogaro da kai ga marayu da marasa galihu su 160, tare da haɗin guiwar gidauniyar Charity.
Kayayyakin da aka rarraba sun haɗa da; Kekunan ɗinki guda 20, mashin mai taya uku guda 20, Injinan nika 20 da ƙurkura da sauran su.
Da yake jawabi a wajen rabon kayayyakin
Gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana shirin a matsayin tallafin dogaro da kai, inda ya jaddada rawar da ƙarfafa gwiwa ko gina al’umma yake takawa wajen dawo da martaba da cigaban ƙasa, musamman mutane masu ƙaramin ƙarfi.
Ya ƙara da cewa, tallafin bai tsaya ga matasa kaɗai ba har da marayu, da tsofaffi, da mata waɗanda mazajen su suka mutu.
Raɗɗa ya kuma buƙaci waɗanda suka amfana da tallafin da su yi amfani da kayayyakin yadda ya kamata, wajen fara ƙananan sana’o’i, don tallafa wa iyalansu, da inganta rayuwarsu ta yau da kullum.
Ya jinjina ma gidauniyar Qatar duba da irin rawar da take takawa a Najeriya musamman a Jihar Katsina, inda ya yi nuni da cewa, aikinsu shi ne babbar shuka wadda take canja rayuwar al’umma daga marasa galihu zuwa mai arziki.
Ita ma da take jawabi, Hon. Jamila Abdu Mani, wacce ta shirya taron, ta bayyana cewa, an bada kayayyakin tallafin ne domin ƙarfafawa marasa ƙarfin gwiwa, inda a lokacin ta shawarci waɗanda suka ci gajiyar tallafin su zama ma su dogaro da kai, da kuma samar da kuɗaɗen shiga ga zuƙatan su, domin gudanar da kyakkyawar rayuwa mai ɗorewa.
Ta kuma yaba da gudunmawar da gidauniyar Qatar ta bayar a baya, a cibiyoyi masu yawa, da suka haɗa da; masallatai, da rijiyoyin burtsatse, waɗanda hakan ya yi matuƙar tasiri ga al’ummomin yankunan jihar.
