An gano ma’aikatan bogi 3,488 a gwamnatin Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

An gano ma’aikatan bogi 3, 488 a cikin ma’aikatan ƙananan hukumomi da na sashin ilimin Firamare dake ƙananan hukumomi 34 a Jihar.

Shugaban kwamitin tantance ma’aikatan ƙananan hukumomi da gwamna Dikko Raɗɗa ya kafa Abdullahi Gagare ya bayyana haka a lokacin da yake miƙa rahoton ga gwamnan jihar a ɗakin taro na gidan gwamnatin jihar.

Ya ce waɗannan ma’aikatan bogi da aka gano na daga cikin guda 50, 172 ɗaukacin ma’aikatan ƙananan hukumomin da aka tantance.

Gagare ya shaidawa gwamnan cewa sakamakon wannan tantancewa da akai, Gwamnatin Jihar Katsina zata rinƙa samun rara, ya ce.

By ukarofi