
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rahotanni daga Jihar Sakkwato sun bayyana cewa, Kwamishinan Ilimi, Farfesa Ladan Ala ya umarci jagororin makaratun sakandare na gwamnati da ke jihar da su dakatar da karɓar kuɗin karatu daga iyayen yara.
Hakan ya biyo naɗa kwamiti da Ma’aikatar Ilimi ta jihar yi domin yin nazari game da ƙorafe-ƙorafen da al’umma ke yi a jihar na kuɗaɗen karatu da ake karɓa a makarantu.
A cewar Kwamishinan, an dakatar da haka ne har zuwa lokacin da kwamitin zai bada rahotonsa akan matakan da suka dace a ɗauka akan lamarin.
A wata takarda daga jami’in yaɗa labarai na hukumar, Ibrahim Mohammed Iya, Kwamishinan ya yi gargaɗin duk shugaban makarantar da aka samu ya saɓa wa umarnin, za hukunta shi kamar yadda doka ta tanada.
Farfesa Ala ya bayyana cewa, kada wani daga cikinsu ya sake neman a biya kuɗin PTA, shiga makaranta, takardar kammala karatu, takardar sakamakon karatu har ma da na ƙungiyar ɗalibai musulmai, wato MSS.
Sauran kuɗaɗen da aka dakatar da karɓa sun haɗa da na takardar shaidar jarrabawa ta BECE, shaidar sakamako da ta kammalawa, takardun rubuta amsar jarrabawa, takardun tantancewa, jarrabawar kammala sakandare (SSCE) da takardun kammala rubuta jarrabawar NECO, NABTEB da NBAIS.
