
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sufeto-Janar na ƴan sanda (IGP), Kayode Egbetokun ya miƙa caki ga iyalai guda 1,574 a ƙarƙashin Shirye-shiryen Insorar rai da Walwalar Iyalai na IGP, waɗanda aka rasa daga shekarar 2015 zuwa 2025 ciki har da wasu haƙƙoƙinsu na tsawon shekaru goma.
Blueprint ta ruwaito cewa, Rundunar ƴan sanda ƙarƙashin Sufeto-Janar Egbetokun ta biya kimamin Naira biliyan 24.2 ga iyalai 9,735 na jami’an da suka rasu a bakin aiki a faɗin Nijeriya.
Da yake magana yayin gabatar da cakin ga iyalan jami’an a Abuja ranar Laraba, Shugaban ƴan sandan ya yi alhini da jajenta wa iyalan mamatan mazansu da matansu bisa sadaukar da kansu wajen hidimar ƙasa.
Ya kuma ci alwashin tabbatar da an yi wa makusanta mamatan adalci, waɗanda suka jima suna jiran hakan daga hukumar, yana mai cewa wannan shi ne karo na 11 da ake gudanar da irin irin shirin tun bayan naɗa shi a muƙamin sufeton.
Ya ƙara da cewa, duk da cewa babu adadin kuɗin da zai iya maye gurbin rashin da aka yi musu, amma suna kokari ganin an samar da yanayi mai kyau na yi wa waɗanda lamarin ya shafa adalci ta yadda hakan zai zama ɓangare na tunawa da jami’an da aka rasa a hukumar.
Kazalika, ya ce suna shirin zamanantar da tsarin biyan domin a riƙa biyansu haƙƙoƙinsu cikin ƙanƙanin lokaci ba tare da samun jinkiri ba.
Da dama daga cikin iyalan sun yaba tare da miƙa godiyarsu ga sufeton isa hoɓɓasa da ya yi cikin al’amuransu.
