An gano Trump na fama da rashin lafiyar jijiya, kumburin ƙafa da kujewar hannu – Tsegumin yanar gizo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Alhamis ne Fadar Shugaban Ƙasar Amurka ta sanar da cewa Shugaban ƙasar, Donald Trump mai shekaru 79 yana fama da rashin lafiya a jijiyoyin ƙafafunsa, lamarin da ya haddasa masa kumburin ƙafa.

Hakan ya biyo bayan raɗe-raɗin da ake yi game da tabon kujewa da hannayensa suka yi da kumbura da ƙafafun nasa suka yi.

Sakatariyar yaɗa labarai ta ‘White House’, Karolina Leavitt ta bayyana cewa an gano halin da Shugaba Trump ya ke ciki ne a kwanan nan a lokacin da aka ga ƙafafun sun fara kumbura.

Ta ce, hakan ya bayyana ne duba da yadda ya ke yawan yin musabaha da jama’a a yayin gaisawa, lamarin da ya sa aka ga alun haka a hannunsu.

A yayin wasan ƙarshe na gasar kofin duniya na ƙungiyoyi wato Club World Cup, an ga gwiwowinsa na hannu sun kumbura a lokacin da ya sanya sabuwar rigar jesi.

Ana ganin hakan ka iya zama barazana ga shugabancin da ya ke yi wa al’ummar ƙasar duba da mawuyacin halin da zai iya shiga a sanadiyyar rashin lafiyar.

By Babaji