An haramta wa fasinja shiga jirgi har abada bayan cin zarafin ma’aikata

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Sama ta Nijeriya (AON) ta sanya dokar hana shiga jiragen sama na tsawon rayuwa ga Comfort Emmanson, wata fasinja da ta ci zarafin ma’aikatan jirgin da ke cikin jirgin Ibom Air daga Uyo, jihar Akwa Ibom zuwa Legas.

An ruwaito cewa lamarin ya kuma kai ga gurfanar da ita a gaban kotu tare da tsare ta a gidan gyaran hali na ƙiriƙiri da ke Legas.

Matakin dai na zuwa ne a wani ɓangare na abin da hukumomin sufurin jiragen sama suka bayyana a matsayin “rashin haƙuri da rashin ɗa’a na fasinja”, wanda ke ƙaruwa a filayen jiragen saman Nijeriya.

Mai magana da yawun Ministan Sufurin Jiragen Sama da Cigaban Jiragen Sama, Tunde Moshood, ya tabbatar da faruwar lamarin a wani saƙo da ya wallafa a shafin ɗ da aka fi sani da Tiwita a ranar Litinin.

Ya bayyana cewa tsare Emmanson ya biyo bayan tuhumar da wata kotu ta yi mata, yana mai gargaɗin cewa irin waɗannan abubuwan za su jawo sakamako cikin gaggawa.

Moshood ya ce, “Ya kamata jam’a su riƙa yin taka-tsantsan, domin an tuhumi fasinjan jirgin da ke kan hanyar Ibom zuwa Uyo zuwa Legas, Comfort Emmanson, a kotu, kuma yanzu haka tana hanyar zuwa gidan yarin Kirikiri,” inji Moshood.

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nijeriya (NCAA) ta kuma nuna cewa a shirye ta ke ta ƙara ɗaukar matakan tabbatar da tsaro a kan fasinjoji masu zafin kai a filayen jiragen sama na Nijeriya, inda jami’ai suka yi nuni da cewa, irin wannan hali na barazana ga lafiyar ma’aikatan jirgin, jin daɗin ma’aikatan, da kuma tsaron lafiyar ma’aikaran jiragen sama baki ɗaya.

A cewar jirgin Ibom Air, rikicin ya fara ne jim kaɗan kafin tashin jirgin daga Uyo lokacin da Emmanson ya ƙi bin ƙa’idojin tsaro da ke buƙatar duk fasinjojin ya kashe wayar hannu yayin tashin jirgi.

Lokacin da wata fasinja da ke zaune kusa da ita ta ɗauki wayar ta kashe, sai Emmanson ya falla mata mari.

Lamarin dai ya ƙara ta’azzara ne bayan ta sauka a Legas, inda ta zargi wani ma’aikacin jirgin wanda ya umurce ta da ta kashe na’urar da zargin yunƙurin yi mata fyaɗe.

Hotunan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta sun ɗauki wani ɓangare na rikicin, inda suka nuna Emmanson tana gardama da ma’aikatan jirgin, daga bisani kuma ta fuskanci jami’an tsaron filin jirgin.

Jirgin Ibom Air ya ce, ɗabi’arta “bai dace ba” kuma yana ya yi babbar barazana ga lafiyar ma’aikatan jirgin, fasinjoji, da kuma jirgin.

Kamfanin jirgin ya mayar da martani ta hanyar sanya mata takunkumi na dindindin a kan duk wani jirginsa.

AON mai wakiltar kamfanonin jiragen sama na cikin gida a Nijeriya, tun daga lokacin ta tsawaita takunkumin a duk faɗin ƙasar, wanda hakan ke nufin ba za a sake barin Emmanson ta yi hau jirgi a kowane kamfanin jiragen sama na Nijeriya ba har tsawon rayuwarta.

By ukarofi