An kama makafin bogi suna safarar yara a Abuja

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wata babbar kotun Abuja a ranar Talata ta bayar da umarnin tsare wasu mata huɗu da ake tuhuma da laifin safarar yara.

Rundunar ‘yan sandan ta gurfanar da matan huɗu ne da laifin haɗa baki da kuma safarar yara.

Matan waɗanda a yanzu ake tuhumar su ne: Precious Silas mai shekaru 30 da Ngozi Unukwuwa mai shekaru 47 da Chisinau Onukwuagha mai shekaru 40 da Favor Ohebegeim mai shekaru 25.

Waɗanda ake tuhumar dukkansu mazauna garin Karimo ne, wata unguwa da ke a yankin kashi uku na Babban Birnin Tarayya Abuja.

A ci gaba da sauraron ƙarar, lauyan masu shigar da ƙara, Donatus Abah, ya shaida wa kotun cewa wazanda ake tuhumar sun yi amfani da wasu yara maza uku ne wajen yin bara a babban birnin tarayya Abuja.

Yaran matasa ‘yan shekaru bakwai, takwas da 12, a cewar Abah.

Mai gabatar da ƙara ya shaida wa kotun cewa waɗanda ake tuhuma huɗu sun kawo yaran ne daga Imo tare da yi musu alƙawarin shigar da su makarantu.

Ya yi zargin cewa matan huɗun sun yi basaja a matsayin makafi ne kuma suka yi amfani da yaran wajen yin bara.

Abah ya ƙara da cewa, gidan Rediyo da Talabijin na kare haƙƙin ɗan Adam ne ya fallasa matan.

Ya kuma shaida wa kotun cewa laifin ya ci karo da tanadin sashe na 14 (b) da na 27 na dokar hana fataucin mutane (Hana) tilastawa da gudanar da mulki na shekarar 2015.

Mai gabatar da ƙara ya ƙara da cewa, laifukan sun kuma saɓa wa sashe na 3(1) da (2) da (3) na dokar kare haƙƙin yara ta 2003.

Sai dai waɗanda a ke tuhuma huɗu sun ƙi amsa laifin da ake tuhumarsu da su.

By ukarofi