Daga CMG HAUSA
Jiya Juma’a 22 ga wata, an kammala taron shekara shekara na dandalin Asiya na Boao mai taken “Annoba da duniya: Ingiza ci gaban duniya da gina makoma tare”, babban sakataren dandalin Li Baodong, ya bayyana yayin taron manema labaran da aka shirya jiya da yammacin ranar cewa, shawarar gudanar da tsaron duniya, babban sakamako ne da aka samu yayin dandalin na wannan karo.
Li Baodong ya kara da cewa, tsaro ya fi muhimmanci yayin da ake ƙoƙarin samun ci gaba, kuma ya dace bil adama su hada kansu a yayin da ake ƙoƙarin tabbatar da tsaro, don haka shawarar gudanar da tsaro a duniya ta samu amincewa daga ɓangaren sassa daban daban na mahalartan taron, yanzu haka shawarar ci gaban duniya da shawarar gudanar da tsaro a duniya za su taka babbar rawa kan aikin gina duniya bayan an shawo kan annobar cutar COVID-19.
Haƙiƙa an shirya taron dandalin ne ƙarƙashin yanayin fama da ƙalubale iri daban-daban wajen samun ci gaba da tabbatar da tsaro a fadin duniya, Li Baodong ya yi tsokaci cewa, mahalarta taron sun cimma matsaya da dama a fannonin ba da kariya ga lafiyar jikin bil adama, da ingiza farfadowar tattalin arzikin duniya, da dakile kalubalen tafiyar da harkokin ƙasa da ƙasa da dai sauransu.
Mai fassarawa: Jamila
