Ƙaddarar Assange ta nuna makircin zaman walwala mai salon Amurka

Daga CMG HAUSA

Kwanan baya kotun birnin Landon ta ƙasar Birtaniya ta amince da mika Julian Paul Assange wanda ya kafa shafin yanar gizo na Wikileaks a ƙasar Amurka a hukumance, lamarin da ya sa aka nuna shakku ko kuma adawa gare shi. Wasu mutane dake goyon bayan Assange su ma sun yi taro a wajen kotun domin yin adawa da ƙudurin. Kana lauyan Assange ya yi nuni da cewa, mai yiwuwa ne za a tsare Assange a gidan yari har tsawon shekaru 175, babban editan shafin yanar gizo na Wikileaks Kristinn Hrafnsson ya bayyana cewa, matakin da Amurka da Birtaniya suka ɗauka ya yi kama da yankewa Assange hukuncin kisan kai.

To mene ne dalilin da ya sa gwamnatin Amurka take mai da hankali kan batun Assange a cikin shekaru sama da goma da suka gabata? Ana ganin dalilin haka shi ne, Assange ya tono bayanai na rashin kunya da suka faru a ƙasar ta Amurka, ƙaddarar Assange ta nuna wa al’ummun ƙasa da ƙasa cewa, babu zaman walwala a Amurka, sai dai aron baki ko dabarun da ‘yan siyasar ƙasar ke amfani da su don yaudaurar sauran ƙasashen duniya.

Shugaban ƙasar Mexico Andrés Manuel López Obrador, ya bayyana a watan Janairun bana cewa, kafin tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya kammala wa’adin mulkinsa, ya rubuta wasika gare shi, inda ya buƙaci ya saki Assange, amma bai samu amsa ba.

Mai fassarawa: Jamila