Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da marigayi Alaafin na Oyo

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

’Yan Nijeriya sun wayi gari da wani labari mai firgitarwa na rasuwar Sarkin Yarbawa, Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi III wanda ya rasu a daren Juma’a 22 ga Afrilu, 2022.

Oba Lamidi Adeyemi III, mai shekaru 83 (marigayi), wanda aka fi sani a Nijeriya a matsayin ɗaya daga cikin manyan sarakuna a ƙasar wanda ya kwashe kusan shekarun Nijeriya akan karagar mulki.

Mulkinsa na Alaafin na Oyo ya fara ne a shekarar 1970 shekaru 10 kacal bayan Nijeriya ta samu ’yancin kai daga Turawan mulkin mallaka na Ingila. Ya shafe shekaru 52 akan karagar mulki, wanda hakan ya sa ba wai kawai Alaafin Oyo mafi daɗewa a kan karagar mulki ba ne, amma har ma ya zama wanda ya fi kowa wane sarki daɗewa a kan karagar mulki a faɗin Nijeriya.

Sarautarsa ​​ta samu nasarori da dama a yabawa, ga abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da marigayi Alaafin na Oyo.

An haifi Alaafin Adeyemi Lamidi Olayiwola Atanda Adeyemi a ranar 15 ga Oktoba, 1938 a cikin gidan sarauta na Alowolodu na shahararren garin Oyo.

Ya zama Alaafin Oyo ne a ranar 18 ga Nuwamba, 1970, inda ya gaji Oba Gbadegesin Ladigbolu I, a lokacin gwamnan Kanar Robert Adeyinka Adebayo, bayan yaƙin basasa. An fi saninsa da Iku Baba Yeye.

A lokacin mulkinsa, Oba Adeyemi ya shugabanci majalisar Obas da sarakunan Jihar Oyo.

A shekarar 1975, shugaban ƙasa Janar Murtala Muhammed ya haɗa da Oba Adeyemi a cikin tawagarsa zuwa aikin hajji.

A shekarar 1980 aka naɗa shi Kansila na Jami’ar Uthman ɗan Fodiyo da ke Sakkwato. Ya riƙe muƙamin har zuwa 1992.

A shekarar 1990 ne shugaban ƙasa Ibrahim Babangida ya naɗa shi Amir-ul-Hajj bisa la’akari da jajircewarsa na tabbatar da addinin Musulunci a Nijeriya.

Alaafin ya auri Ayaba Abibat Adeyemi, uwar gidansa. Duk da haka, yana da mata kusan goma sha biyu, waɗanda ya halarci taron tare da su.

Matan nasa sun haɗa da Ayaba Rahmat Adedayo Adeyemi, Ayaba Mujidat Adeyemi, Ayaba Rukayat Adeyemi, Ayaba Folashade Adeyemi, Ayaba Badirat Ajoke Adeyemi, Ayaba Memunat Omowunmi Adeyemi, Ayaba Omobolanle Adeyemi, Ayaba Moji Adeyemi, Ayaba Anuoluwa, Adeyemi Adeyelami da kuma Ayaba Anuoluwapo Adeyela.

Ko da ya ke ba a tabbatar da adadin ’ya’yan nasa ba, Alaafin yana da ’ya’ya da dama, daga cikinsu akwai ’ya’ya uku.

Da Rasuwar Alaafin Adeyemi, yanzu lokaci ne na Majalisar Mulkin Agunloye don samar da Sarkin Oyo mai zuwa. Marigayi Adeyemi, Alaafin Ladigbolu, ya fito ne daga gidan Agunloye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *