An kashe sufeton ‘yan sanda a hatsaniya da ‘yan acaɓa a Jihar Filato

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wani sufeton ‘yan sanda da ke ofishin ‘yan sanda na ‘C’’ dake Jos ta Arewa a Jihar Filato, Insifekta Mohammed Kile Tahir, ya rasa ransa a daren Asabar, 1 ga Maris, 2025.

An tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:30 na dare a bayan otal ɗin Moonshine dake kusa da titin Atili yayin wata arangama tsakanin ‘yan sanda da ke sintiri na yau da kullum da ‘yan okada da masu tuka keke.

An ce ‘yan sandan sun killace hanyar ne domin “yin bincike”.

Maimakon bin ’yan ta’adda, ‘yan okada da masu tuƙa keke Napep, waɗanda su ma ke karya dokar hana zirga-zirga a lokacin, sun yi zargin cewa ‘yan sanda sun shagaltu da karɓar N50, 100, da 1,000 daga hannunsu.

‘Yan okada da masu tuƙa Napep, a wannan sa’ar, sun kuma karya dokar gwamnatin jihar, wadda ta ce su dakatar da ayyukansu da ƙarfe 6 na yamma.

Sun kuma yi iƙirarin cewa ‘yan sanda za su riƙa fakewa a wani wuri mai duhu a irin wannan sa’o’in da ba su dace ba, tare da toshe hanyoyi, da karɓar kuɗi daga hannun masu ababen hawa da ba su ji ba su gani ba.

Wani ɗan acaɓa da lamarin ya harzuƙa, da sauri suka tara mambobinsu, inda suka zo suka gangaro kan jami’an ‘yan sandan, suna jifansu da duwatsu, da sanduna, da adduna. Hakan ya sa Sufeto ya samu munanan raunuka, inda aka garzaya da shi wani asibiti da ke kusa, inda aka tabbatar da rasuwarsa washegari.

Wata sigar ta bayyana cewa jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA ne ke gudanar da aikin neman masu fataucin miyagun ƙwayoyi a cikin sa’o’in da suka wuce.

Wannan sigar ta bayyana cewa, a yayin gudanar da aikinsu, jami’an ‘yan sanda na “C” Dibision, waɗanda ke sintiri na yau da kullum, sun bi ta wannan hanya.

Wannan sigar ta yi nuni da cewa waɗanda ake zargin masu safarar miyagun ƙwayoyi ne suka haɗa kansu da jami’an NDLEA kuma ba ‘yan sanda ba ne.

Da aka tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sanda (PPRO) DSP Alfred Alabo bai amsa kiran da aka yi masa ba.

By ukarofi