An kusa magance matsalar ƙarancin shaguna a Kasuwar Zamani ta Bichi — Shugaban Kasuwa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Kasuwar Zamani ta ƙaramar Hukumar Bichi, Alhaji Garba Tukur, ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba sauran ’yan kasuwar da har yanzu ba su mallaki shaguna ba za su samu nasu wuraren kasuwanci.

Alhaji Garba Tukur ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da wakiliyar yaɗa labarai ta yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo, a wata ziyara ta gani da ido da aka kai kasuwar domin duba ayyukan gina shaguna da ake ci gaba da yi a sassa daban-daban na kasuwar.

Da yake jawabi, shugaban kasuwar ya ce jinkirin da aka samu wajen rabon shaguna ga wasu ’yan kasuwa ya samo asali ne daga ci gaba da aikin tantance haƙiƙanin masu kasuwanci da ake gudanarwa, domin tabbatar da cewa an bai wa waɗanda suka cancanta haƙƙinsu.

Ya bayyana cewa bayan zamanantar da kasuwar da aka yi tare da shimfiɗa hanyoyin mota da magudanan ruwa domin samar da tsafta da tsaro, adadin shagunan da ake da su ya ragu idan aka kwatanta da yadda kasuwar take a baya.

“An sake fasalin kasuwar ne domin ta kasance cikin tsari da tsafta. Hakan ya sa aka samar da hanyoyi da magudanan ruwa, wanda ya rage yawan wuraren da za a gina shaguna. Duk da haka, shagunan da aka gina a ƙasa da kuma bene ba su kai kashi ɗaya bisa uku na faɗin kasuwar ba. Amma ina tabbatar wa da jama’a cewa nan da mako uku, in Allah Ya yarda, za a ga ’yan kasuwa suna gudanar da harkokinsu a sabbin shagunan,” inji Alhaji Garba Tukur.

Ya ƙara da cewa, ba za a ɗauki lokaci mai tsawo ba kafin a kammala sauran shagunan da ake shirin ginawa a filin tashar da ke makwabtaka da kasuwar domin amfanin sauran ’yan kasuwa.

“ɗan Majalisar ya riga ya tattauna da ɗan kwangilar da zai ci gaba da aikin. Saboda haka, ba da jimawa ba za a fara gina sauran shagunan da suka rage, kuma kowane ɗan kasuwa zai samu nasa shagon da yardar Allah,” inji shi.

Har ila yau, shugaban kasuwar ya yabawa ƙoƙarin ɗan majalisar, yana mai cewa ba gina kasuwar kaɗai ya tsaya yi ba, har ma yana aiwatar da wasu muhimman ayyukan raya ƙasa da za su amfani al’ummar yankin.

A ƙarshe, ya yi wa ’yan kasuwar albishir da wani shiri na tallafin jari da ake shirin ƙaddamarwa domin bunƙasa kasuwancinsu.

“Baya ga wannan, ɗan majalisar ya umarce mu da mu tantance haƙiƙanin ’yan kasuwar da za su amfana da tallafin jari. Nan da kwanaki talatin, in Allah Ya yarda, za a fara rabon tallafin,” inji Alhaji Garba Tukur.

By ukarofi

Leave a Reply