Daga ABDULLAHI SANI DOGUWA a Kano
Wani ɗan kishin ƙasa kuma mai fafutukar ci gaban al’umma, Dakta Jibril Gambo Hadejia, ya bayyana damuwarsa kan rikice-rikicen da ke faruwa a wasu ƙasashen da Nijeriya ke mu’amala da su, musamman a fannin samar da muhimman kayayyaki kamar man fetur da siminti.
Ya ce waɗannan rikice-rikice na da tasiri kai tsaye wajen hauhawar farashin kayayyakin, duk da cewa Nijeriya na da yalwar rijiyoyin man fetur da kuma masana’antun siminti.
Dakta Gambo ya bukaci masu ruwa da tsaki a fannin man fetur da na siminti da su ɗauki matakan da za su rage tsadar kayayyakin, domin saukaka rayuwa ga ‘yan kasa, musamman masu sana’o’in hannu da ƙananan ‘yan kasuwa.
Ya kara da cewa rage farashin wadannan kayayyaki zai taimaka matuka ga masu sana’ar sarrafa bulo na siminti da sauran kananan sana’o’i, ta yadda za su iya dogaro da kansu tare da samar da ayyukan yi ga matasa, wanda hakan zai taimaka wa gwamnati wajen rage rashin aikin yi.
Dakta Jibiril Gambo ya bayar da misalin yadda matasa da dama a Hadejia ke samun abin yi ta hanyar harkar sarrafa bulo na siminti, inda ya ce hakan ya taimaka wajen rage zaman kashe wando a tsakanin matasa.
Haka kuma, ya jaddada bukatar da ke akwai ga masu hannu da shuni da su rika amfani da damarsu wajen kafa cibiyoyin horas da al’umma sana’o’in dogaro da kai.
Wasu daga cikin matasan da ke aiki a bangaren sarrafa bulon siminti sun bayyana godiyarsu ga Dakta Jibiril Gambo bisa irin goyon bayan da yake ba su, tare da kira ga hukumomi da su kara tallafa musu domin bunkasa harkokinsu na yau da kullum.
