Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban INEC Amupitan na kitsa maƙarkashiyar murkushe duka jam’iyyun banda APC kadai, muna kira da a tsige shi – ADC
Jam’iyyar ADC ta rubuta saƙo zuwa ga alƙalin alƙalai ta Nijeriya, Kudirat Kekere-Ekun, inda ta buƙaci da ta sa baki wajen gaggauta yanke hukunci kan rikicin shugabanci da jam’iyyar da ke gaban kotun ƙoli.
A cikin wasiƙar da aka aike wa da ofishin alƙalin alƙalan a ranar Talata, lauyan ADC, S. E. Aruwa (SAN), ya ce, ci gaba da jan ƙafa da aka samu ka iya jefa jam’iyyar cikin halin rasa damar shiga a dama da ita a harkokin zaɓen 2027.
“Damar da ADC ke da ita na shiga a dama da ita a zaɓen 2027 ya dogara ne da gaggauta yanke hukunci da ke gaban kotu,” in ji wasiƙar.
Rikicin shugabanci a jam’iyyar ya shafi tsagin da David Mark ke jagoranta da tsagin Nafiu Bala wanda ke iƙirarin zama halastaccen shugaban ADC wanda hakan ya kai ga ɗaukaka ƙara. Kotun ɗaukaka ƙara ta ba da umarnin komawa matsayar da ake a baya kafin fara rikicin. Sakamakon haka, INEC ta dakatar da kallon kowanne ɓangare a matsayin halastaccen shugaba.
Sai dai dukkan ɓangarorin sun yi watsi da matakin INEC a yayin da kowanne ɓangare ke ci gaba da iƙirarin zama halastaccen shugaban ADC.
Wannan lamari ya kai ga an dangana da kotun ɗaukaka ƙara a ranar 22 ga watan Afirilu.
Jam’iyyar ta ce wannan giɓi da ake da ita ka iya zama tarnaƙi wajen ba ta damar shiga a dama da ita la’akari da jadawalin zaɓen da INEC ta fitar na shekarar 2027.
A cewar INEC, lallai ne dukkan jam’iyyun siyasa su yi zaɓen fidda gwani zuwa ranar 30 ga watan Mayu.
“Sai dai ba tare da an yanke hukunci ba, a cikin kwanaki uku masu zuwa daga ranar da aka fitar da wannan wasiƙa, ADC na cikin barazanar rashin samun damar shiga a dama da ita a harkokin zaɓen 2027,” ta faɗa.
Lauyoyi sun ce kowanne irin mataki da jam’iyyar za ta ɗauka ya ta’allaƙa ne da sakamakon hukuncin Kotun ƙoli, suna masu jaddada cewa jinkirin da ake samu ka iya yin illa mai yawa ga ADC.
