Shari’ar yunƙurin juyin mulki: Shaidu sun bayyana yadda aka raba miliyoyin kuɗaɗe

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

An fara sauraron shari’ar da ake yi cikin gaggawa kan wasu mutane shida da ake zargi da shirya juyin mulki a kan gwamnatin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, inda wata muhimmiyar shaida daga rundunar soji ta bayyana wa kotu cewa an raba sama da Naira miliyan 600 domin aiwatar da shirin, tare da alaƙanta tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, Timipre Sylva, da wasu bayanan kuɗi da aka gano a bincike.

Shaidar, wani jami’i daga rundunar ’yan sandan sojin Nijeriya, wato Nigerian Army Corps of Military Police (NACMP), wanda aka ɓoye sunansa da laƙabin “AAA”, ya bayyana a gaban kotu yadda aka gano shirin juyin mulkin da kuma irin bayanan da aka tattara.

Ya ce, binciken ya samo asali ne bayan tsohon Babban Hafsan Sojin ƙasa, Janar O.O. Oluyede, ya samu bayanan sirri da ke nuna cewa Kanar M.A. Ma’aji tare da wasu jami’ai da fararen hula na shirin kifar da gwamnati.

A cewarsa, bayan tantance bayanan da aka samu, an tabbatar da ingancinsu, lamarin da ya sa aka umarci ƙungiyar bincike ta fara aiki. Daga bisani aka kama Kanar Ma’aji, inda aka ƙwato wayarsa ta Samsung Galaɗy tare da gudanar da bincike a gidansa.

Shaidar ta ce, an gano wata takarda a cikin littafin rubutu (jotter) da ke ɗauke da tsare-tsaren aiki, sunayen manyan jami’an gwamnati da kuma jerin mutanen da ake zargin an shirya kashe su idan an aiwatar da juyin mulkin.

“Mun kuma gano wasu bayanai kan sauye-sauyen siyasa da tsarin gwamnati da za a yi bayan juyin mulkin,” inji shaidar.

Binciken fasaha da aka yi kan wayar Kanar Ma’aji, a cewar shaidar, ya bayyana alaƙa mai ƙarfi tsakanin shi da wasu daga cikin waɗanda ake tuhuma, tare da gano hanyoyin zirga-zirgar kuɗi da ke danganta su da tsohon gwamna Timipre Sylva.

Haka kuma, ya bayyana cewa an gano wasu kalmomin sirri da masu shirin ke amfani da su wajen sadarwa, da kuma yadda aka riƙa biyan kuɗaɗe ga wasu daga cikin waɗanda ake tuhuma domin ciyar da shirin gaba.

Shaidar ta ƙara da cewa, bincike ya gano wata kamfani mai suna “Purple Wave” wadda ake zargin an yi amfani da ita wajen karkatar da kuɗaɗe domin tallafa wa shirin juyin mulkin. Ya ce Hukumar EFCC ce ta samar da bayanan asusun kuɗin kamfanin.

Daga cikin kuɗaɗen da aka gano, akwai ma’amaloli da dama da suka kai miliyoyin naira, ciki har da miliyan N100, N50 da N80 a ranakun daban-daban tsakanin Satumba da Oktoba 2025, waɗanda bincike ya nuna an karkatar da su domin shirin juyin mulki, duk da cewa an bayyana wasu daga cikinsu da wasu dalilai daban.

Shaidar ta kuma ce an gudanar da taruka da dama a wurare irin su gidajen haya da otel-otel a Abuja, inda ake tattauna buƙatar sauya gwamnati tare da tsara yadda za a aiwatar da shirin, ciki har da kama muhimman hanyoyi da kai hare-hare kan wasu wuraren soji.

“Sun raba mukamai a tsakaninsu, tare da tsara sabbin hukumomi da kuma waɗanda za a haɗa bayan juyin mulkin,” inji shaidar.

Haka kuma, ya bayyana cewa an sayo wasu motoci da aka shirya canza su domin ayyukan farmaki, waɗanda daga bisani aka gano su a shagunan gyara.

A yayin shari’ar, lauyan gwamnati, Daraktan Shari’ar Tarayya Rotimi Oyedepo, ya gabatar da hujjoji daban-daban ciki har da takardun banki da bayanan wayar salula, yayin da Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta amince da gabatar da wasu daga cikin hujjojin.

Kotun ta kuma saurari shaidu daga jami’an bankuna daban-daban da suka gabatar da bayanan asusun waɗanda ake zargi da hannu a lamarin.

Daga ƙarshe, Mai shari’a ta ɗage ci gaba da sauraron ƙarar zuwa ranakun 4 da 5 ga watan Mayu, inda ake sa ran wata sabuwar shaida za ta ci gaba da gabatar da bayanai a gaban kotu.

By ukarofi