’Yan sanda sun cafke mutum shida bayan rikicin daba a kasuwar Farm Centre ta Kano

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta tabbatar da cafke mutane shida da ake zargi da hannu a rikicin ’yan daba da ya rikiɗe zuwa harin da aka kai a babbar Kasuwar Wayoyi ta Farm Centre da ke Kano, lamarin da ya jefa kasuwa cikin tashin hankali tare da haddasa asarar kayayyaki masu yawa.

A cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar Talata, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da tsakar rana a ranar Litinin, inda wasu matasa da ake zargi da ɗaukar makamai suka kutsa cikin kasuwar tare da yin sata da kuma lalata dukiyoyin ’yan kasuwa da abokan ciniki.

Rundunar ta bayyana cewa rikicin ya samo asali ne daga wani kiran gaggawa da ya nuna cewa wasu ’yan daba sun shirya yin artabu a yankin Gyadi-Gyadi, wanda ke kusa da kasuwar.

“An tura jami’an sintiri nan take, inda suka tarar da rikici na gudana. Har ma an lalata motar asibiti a lokacin tashin hankalin,” inji CSP Kiyawa.

Ya ƙara da cewa bayan haka, ’yan daban sun sake taruwa suka kai hari kan jami’an tsaro da duwatsu da makamai, amma aka daƙile su cikin nasara.

“Daga baya sun gudu zuwa Kasuwar Farm Centre inda suka yi ƙoƙarin shiga shaguna domin satar kaya, amma jami’an tsaro suka daƙile su tare da ƙarin ƙarfafawa daga hedikwata,” inji shi.

Sanarwar ta ce, an kama mutane shida yayin da aka sake dawo da zaman lafiya a wuraren da abin ya shafa, yayin da ake ci gaba da farautar sauran waɗanda suka tsere.

Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya yabawa jami’an tsaro bisa gaggawar da suka yi wajen daƙile rikicin, yana mai cewa hakan ya hana abin ya ƙara rikiɗewa zuwa babban rikici.

Ya kuma gargaɗi jama’a, musamman iyaye da masu kula da matasa, da su riƙa hana ’ya’yansu shiga ayyukan daba da tayar da fitina a cikin al’umma.

Rundunar ta ce, za ta ci gaba da bincike domin gano duk waɗanda ke da hannu, ciki har da masu ɗaukar nauyin ayyukan tashin hankalin.

By ukarofi