Akpabio ya ayyana kujerar Sanata Jimoh a matsayin wacce babu mai ita

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ayyana kujerar sanatan Ondo ta Kudu a matsayin wacce babu mai ita, bayan naɗin Sanata Jimoh Ibrahim a matsayin wakilin dindindin na Nijeriya a Majalisar ɗinkin Duniya.

Rahotanni sun bayyana cewa Akpabio ya sanar da wannan mataki ne a zaman majalisar na ranar Talata, inda ya ce matakin ya fara aiki nan take bisa tanadin Kundin Tsarin Mulkin ƙasa.

A cewarsa, wannan sauyi ya biyo bayan sabon muƙamin diflomasiyya da aka ba Ibrahim, wanda ya wakilci mazaɓar Ondo ta Kudu a ƙarƙashin jam’iyyar APC kafin naɗin nasa.

Shugaban majalisar ya kuma umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) da ta shirya zaɓen cike gurbi cikin kwanaki 30 domin maye gurbin kujerar da ta zama fanko.

Bisa kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999 (da aka yi wa kwaskwarima), wajibi ne Majalisar Dattawa ta sanar da hukumar zaɓe duk lokacin da aka samu gurbi a cikinta, domin fara shirin gudanar da sabon zaɓe.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ganin sauye-sauyen mukamai a fagen siyasa da diflomasiyya na ƙara tasiri a tsarin mulkin ƙasa, musamman gabanin babban zaɓen 2027.

By ukarofi