Jinkiri ko soke tashin jirgi: FCCPC ta fayyace haƙƙin fasinjoji a Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD

Hukumar Kula da Gasa da Kare Haƙƙin Masu Amfani da Kayayyaki ta Tarayya (FCCPC), ta bayyana cewa fasinjojin jiragen sama suna da haƙƙin samun kulawa ta musamman idan jirginsu ya jinkirta ko aka soke shi ba zato ba tsammani.

Daraktan Harkokin Sadarwa na hukumar, Ondaje Ijagwu, ya bayyana hakan a wani shiri na gidan talabijin na Channels, inda ya jaddada cewa akwai ƙa’idoji da ke wajabta wa kamfanonin jiragen sama taimaka wa fasinjoji a irin waɗannan lokuta.

A cewarsa, idan jirgi ya jinkirta, dole ne a ba fasinjoji abin sha ko abinci mai sauƙi, sannan idan jinkirin ya ƙaru, a ba su kuɗin katin waya domin su iya tuntuɓar iyalansu ko waɗanda suke jira. Ya ƙara da cewa doka ta ɗauki irin wannan jinkiri a matsayin wani yanayi na damuwa ga fasinjoji, wanda ke wajabta ƙarin kulawa.

Game da soke jirgi kwatsam, Ijagwu ya ce a irin wannan yanayi, kamfanonin jiragen sama na iya zama wajibi su samar da sufuri da ma masauki ga fasinjoji, musamman idan filin jirgin yana da nisa da birni ko kuma lokacin ya yi tsawo.

Wannan bayani na zuwa ne a daidai lokacin da harkar sufurin jiragen sama ke fuskantar ƙalubale a ƙasar nan, inda ake samun jinkiri da soke jirage akai-akai. A wasu filayen jiragen sama, ciki har da Nnamdi Azikiwe International Airport, an ga fasinjoji da dama sun makale ba tare da wani taimako ba.

Rahotanni sun nuna cewa hauhawar farashin man jiragen sama na Jet A1 ne ke haddasa wannan matsala, inda farashin ya tashi daga kusan N900 zuwa sama da N3,300 cikin ɗan lokaci kaɗan. Wannan ya jefa kamfanonin jiragen sama cikin matsin lamba, har ma wasu suna barazanar dakatar da aiki.

Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama da Raya Sararin Samaniya, Festus Keyamo, ya yi nuni da yiwuwar ƙarin kuɗin tikitin jirgi domin ceto kamfanonin daga durƙushewa.

Duk da haka, FCCPC ta jaddada cewa duk wata matsala da kamfanonin jiragen sama ke fuskanta ba ta cire musu alhakin kare haƙƙin fasinjoji ba, tare da tabbatar da cewa ana bin ƙa’idojin da suka tanada.

By ukarofi