Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wani dattijo a gabashin ƙasar Indiya ya girgiza ma’aikatan banki da abokan hulɗa bayan ya tono gawar ’yar uwarsa domin tabbatar da mutuwarta da kuma samun damar karɓar kuɗin da ke asusunta.
Lamarin ya faru ne a ranar Litinin a yankin Malipasi da ke gundumar Keonjhar a jihar Odisha, kamar yadda rahotanni suka nuna.
A wani saƙo da ya wallafa a ɗ, bankin Indian Overseas ya bayyana cewa ba a nemi mutumin ya kawo gawar ‘yan uwar shi da ta mutu ba.
Mutumin mai suna Jitu Munda daga kauyen Dianali ya je reshen bankin Odisha Grameen da ke yankin Patana domin cire kusan rupiya 20,000 daga asusun ’yar uwarsa Kalara Munda, wadda ta rasu.
Sai dai ma’aikatan bankin sun buƙaci takardun da ake buƙata da za su nuna tabbas cewa ta mutu kafin su aiwatar da buƙatar.
A wani mataki mai ban mamaki, Munda ya tono kwarangwal ɗin ‘yar uwarsa ya kai shi bankin a matsayin hujjar mutuwarta, abin da ya razana duk wanda ke wurin.
“Na gaya musu ta rasu, amma ba su saurare ni ba. Suna cewa sai na kawo mai asusun kafin a ba ni kuɗin. Saboda takaici ne na tono kabarin na kawo kwarangwal ɗinta domin tabbatar musu cewa ta rasu,” inji shi.
Lamarin ya sa jami’an ‘yan sanda daga yankin Patana suka kai ziyara bankin bayan samun rahoto, wani jami’in ‘yan sanda, Kiran Prasad Sahu, ya ce hakan ya nuna ba a fahimci juna ba.
“Bai fahimci ma’anar magaji ko wanda zai karɓi kuɗi a asusu ba bayan mutuwar mai shi. Ma’aikatan bankin sun kasa bayyana masa yadda ake karɓar kuɗi daga asusun mamaci,” inji Sahu.
Bayan shigar ‘yan sanda, ma’aikatan bankin sun tabbatar wa Munda cewa za a taimaka masa wajen bin hanyoyin doka domin samun kuɗin.
Daga bisani, an mayar da gawar aka sake binne ta a kabari a gaban jami’an ‘yan sanda kuma an bi hanyoyin da suka dace wajen ba shi kuɗin.
