Mutane sun nemi afuwar macen da suka zarga da maita a Kaduna

Spread the love

Daga ZUBAIRU JIBIA a Abuja

Wasu mazauna yankin Kinkinau da ke a garin Kaduna sun janye zargin da suka yi wa wata mace mai suna Fatima Muhammad, na cewa ita ‘mayya’ ce tare da neman afuwarta a gaban kotu.

Mutanen, waɗanda suka haɗa da Mustapha Alhassan, wanda aka fi sani da Babangida Bangis, Maman Babangida da kuma Maman Amina, sun bayyana hakan ne a gaban kotun da ke zamanta a titin Ibrahim Taiwo Road a garin Kaduna.

A cikin bayanin da suka yi, sun amince cewa zargin da suka yi wa Fatima Muhammad ba gaskiya ba ne, kuma ba su da wata hujja da za ta tabbatar da hakan.

Sun kuma roƙi gafarar Fatima Muhammad da ma al’ummar Kinkinau baki daya bisa wannan zargi da suka ce ya ɓata mata suna da mutunci a idon jama’a.

Bugu da ƙari, sun yi kira ga jama’a da su guji yaɗa irin waɗannan zarge-zarge ba tare da hujja ba, domin hakan na iya janyo matsala tare da lalata zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Lamarin dai ya janyo hankalin mazauna yankin, inda da dama ke kallon matakin a matsayin darasi kan illar yaɗa jita-jita da zargi marar tushe a cikin al’umma.

By ukarofi