An nemi manoma su rungumi noma a matsayin sana’a

Daga SANI AHMAD GIWA

An yi kira ga manoman jihar Kano da su himmatu wajen aikin noma da kiwo, kuma su mayar da shi na kasuwanci maimakon na ci kawai.

Malam Issac Eni, wanda masani ne akan harkokin kasuwancin noma, kuma babban jami’in harkokin kasuwanci shi ne ya yi wannan kira a wani taron masu ruwa da tsaki da cibiyar Sasakawa tata shirya a jihar Kano.

Cibiyar ta Sasakawa Global 2000 SAA ta shirya taron ne ga ɗaukacin manoma da ke kan tsarin nan na bunƙasa harkokin noma da kiwo na gwamnatin jihar Kano wanda ake yi wa laƙabi da KSADP a cibiyoyi biyar na jihar Kano waɗanda suka haɗa da Bichi, Gwarzo, Wudil, Kura da Rano.

Shirin KSADP shiri ne da Bankin Addininn Musulunci da ke jidda wato ISDB ya ɗauki nauyi tare da tallafin Cibiyar Bunƙasa Rayuwa (LLF) da Asusun  Bunqasa Cigaban Musulunci (ISDFD) domin ganin an dawo da ruhin noma da kiwo da ke faɗin jahar Kano.

Eni ya buƙaci manoman da su yi amfani da irin dabarun  da noman na zamani da kuma hanyoyin kasuwanci na amfani gona da hukumar ta Sasakawa ta ke koya musu, ya kuma ja hankalin su cewa matuƙar sun yi riƙo da sababbin dabaru da ilimin da ake ba su na noman to ba shakka za su fita daga ƙangin talauci da suke ciki.

A nasu ɓangaren, mahalarta taron sun bayyana jin daɗi tare da bada tabbaci akan za su yi amfani da irin abubuwan da suka koya a cikin shirin na bunqasa noma da kiwo a Jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *