2023: Katinka shi ne makaminka, cewar Sa’adu Gulma

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi

Shugaban Jam’iyyar APC Arewa na jihar Legas, Alhaji Sa’adu Yusuf Dandare Gulma ya yi kira ga ’ya’yan jam’iyyar APC musamman ’yan Arewa mazauna kudancin ƙasar nan da su tabbatar da kowa ya yi rajista ta jam’iyya da kuma jifa ƙuri’a.

Ya yi wannan kiran ne ranar Laraba da ta gabata a ofishinsa inda ya karɓi baƙuncin shugabannin gamayyar ƙungiyoyin matasan jihohi goma sha tara na arewacin ƙasar nan.

Alhaji Sa’adu Gulma ya ce, yin rajista ga ɗan siyasa wajibi ne saboda duk yadda ka ke son mutum idan ranar zaɓe ta zo ba ka da katin jifa ƙuri’a ba ka da wani amfani a wajensa saboda haka ya zama wajibi ga kowanensu ya tabbatar da cewa yana da katin jifa ƙuri’a saboda shi ne makamin da zai yi tinƙaho da shi ranar zaɓe.

Ya bayyana cewa, idan aka cire Yarbawa a jihar Legas, ba wata al’umma da ta kai yawan ‘yan Arewa, hakazalika a siyasance ba ƙaramin gudummawa al’ummar Arewa ke bayarwa ba ga jihar Legas musamman matasa.

Ya kuma yi kira ga matasan da su haɗa kai waje ɗaya don a gudu-tare a tsira-tare musamman wajen samun romon dimokuraɗiyya, sannan kuma su kasance masu bin doka da oda kuma su guji duk wani abu da zai iya kawo tashin hankali a cikin al’umma su kuma a matsayin su na shugabanni a shirye su ke na ganin sun kwato wa haƙƙin duk wanda aka zalunta muddin yana bisa gaskiyarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *