Sojoji sun musunta jita-jitar Injiniyoyinsu na gina ruga a Inugu

Daga AMINA YUSUF ALI

A ranar Larabar da ta gabata ne, Rundunar sojojin tawaga ta 82 suka ƙaryata wani labari da yake ta zazzagawa a kan cewa Sojojin Nijeriya suna gina gidajen makiyaya wato ruga a cikin garruwan Ochima da Affa da ke ƙananan hukumomin Igbo-Etiti da Udi dukkansu a jihar  Enugu.

Tawagar sojojin ta ambaci labarin da labarin ƙanzon kurege, kuma maras tushe balle makama.

Wannan bayani dai yana ƙunshe ne a cikin wata takarda da rundunar ta wallafa, wacce mataimakin riƙo ga jami’in hulɗa da jama’a na sojojin Najeriya wato Manjo Abubakar Abdullahi ya sanya wa hannu. Abdullahi ya bayyana tsananin damuwarsa a kan yadda aka yi ta yaɗa labarin a wata haramtacciyar tashar rediyo.

Inda ya ƙara da cewa: “Kamar yadda aka dinga yaɗa wannan labari maras tushe daga wata haramtacciyar kafar labari, ya kamata a yi bayani a fito da abin sarari yadda mutane za su fahimta”.

A don haka a cewar su, suke ƙara jaddada cewa, Injiniyoyin sojin Nijeriya ba sa gina gidajen ruga a ko ma wanne ɓangare ne ma a Nijeriya. Abinda suka sani dai kawai shi ne, Rundunar ta sojin tana gina wasu wuraren horas da sojoji a tsakanin garuruwan Ochima da Affa da suke cikin ƙananan hukumomin  Igbo-Etiti da Udi na jihar Inugu.

A dai cikin takardar, an ƙara da cewa, da zarar an gama wancan gini, za a sanya sojoji a ciki su dinga amsar horaswa domin su samu ƙwarewar da za su cigaba da ba da tsaro ga ‘yan kudu maso gabacin ƙasar nan masu bin doka.

Inda suka ce, baya ga wannan, duk wani labari da aka samu, labarin ƙarya ne na neman tunzura al’ummar Nijeriya su yi bore ga sojojin.

Da wannan suka ce suna shawartar al’umma da su yi watsi da wancan labari da suka samo daga waccan haramtacciyar kafa ta yaɗa. Domin rundunar sojoji tana nan yadda aka santa wajen haɗa kan al’umma da kauce wa abinda ya shafi ɓangarancin addini ko ƙabilanci.

Kuma za su cigaba da sauke haƙƙin da ya rataya a wuyansu kamar yadda ya zo a kundin tsarin mulkina ƙasar nan, ba tare da wariya ba ko tsoma hannu a harkar siyasa, domin samun cigaba da bunƙasr arzikin ƙasa.