An rantsar da shugabannin LPG na Kano

Spread the love


Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Ƙungiyar masu sana’ar sayar da iskar gas ta ƙasa reshen Jihar Kano, ta rantsar da sababbin shugabannin ƙungiyar Liquefied Petroleum Gas Retailers, ƙarƙashin shugabancin Kwamared Omede Mohammed, wanda zai ja ragamar ƙungiyar LPG ta ƙasa reshen Jihar Kano a wannan lokaci a wani taro da aka yi a makon da ya gabata a birnin Kano.
A jawabinsa bayan rantsuwar Omede Mohammed ya yi alƙawarin shugabanci nagari daidai gwargwadon iko a matsayin wanda aka ɗorawa nauyin shugabancin, kuma zai haɗa kai da ɗaukacin shugabanni da shugabannin wannan ƙungiya domin yin aiki na cigaban ‘yan ƙungiyar da sauran al’ummar Kano da Nijeriya baki ɗaya.
Taro ya samu halarar manyan jagororin wannan ƙungiya a matakin ƙasa da jiha, irinsu Alhaji Yusuf Salisu Gulu, Alhaji Yunusa M Giɗaɗo, babban jami’i a wannan ƙungiya a Kano.
Haka kuma akwai Alhaji Sabo Dahiru Muhammad da Francis Nncho da dai sauran shugabannin ƙungiyar da kuma shugabanta na ƙasa wanda dukkaninsu, suka yi jawabi kan muhimmancin wannan ƙungiya wajen samarwa ɗimbin matasa aikin dogaro da kai da ke bunƙasa tattalin arziƙinsu, da jihar su, da ƙasarsu.

By ukarofi