Muna da kyakkyawar alaƙa da tsohon hadimin shugaban ƙasa kan yaɗa labarai – Tsohon Shugaban NUJ na Kano

Spread the love


Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano


An bayyana cewa akwai kyakkyawar alaƙa mai dogon tarihi tsakanin ƙungiyar ‘yan jaridu ta ƙasa reshen jihar Kano da tsohon mataimakin shugaban ƙasa na musamman kan harkar yaɗa labarai a zamanin shugaban Nijeriya Marigayi Alhaji Umar Musa Yaradua da Goodluck Ebele Jonathan wanda ya shekara takwas a wannan matsayin na mataimaki na musamman akan harkar yaɗa labarai wato Malam Yakubu Musa, wanda fittacen ɗan jarida ne.
Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Malam Abbas Ibrahim tsohon shugaban ƙungiyar yan jaridu NUJ na jihar Kano kuma mataimakin sakataren ƙunigyar kwadago NLC na ƙasa reshan jihar Kano kamar yadda ya bayyana ga manema labarai a lokacin da yan jaridu Kano da na ƙasa da yan kwadago da sauran jamian gwamnatin, yan siyasa, Malamai da sauran alumma suka yi dandazon wurin walimar da daurin auren yar tsohon mataimakin shugaban ƙasa kan yaɗa labarai Malam Yakubu Musa na yarsa mai suna, Sumayya Yakubu Musa wanda aka gabatar a ranar lahadin nan da ta gabata.
Haka zalika Malam Abbas Ibrahim tsohon shugaban NUJ kuma mataimakin sakataren NLC reshen jihar Kano ya ce mahaifin Sumayya Yakubu Musa sun daɗe da shi a Legas tare da kawun sa Malam Sani Zooro tsohon shugaban ƙungiyar ‘yan jaridu na ƙasa kuma tsohon babban edita na rikunonin jaridun National Concord wanda suka yi aiki a Nijeriya wanda suka yi aiki da shi a Legas a shekarun baya kuma wani abun farin ciki da jin daɗi da ni’imar Ubangiji shi ne Allah ya sa sun halarci ɗaurin auren Sumayya Musa yau kuma ga shi da shi aka yi ɗaurin auren ‘yar su kuma jikarsu Sumayya Yakubu Musa, wanda ya ce sun gode wa Ubangiji.
Haka shi ma Malam Yakubu Musa ya yaba wa ƙungiyar ‘yan ƙwadago ta ƙasa reshen Jihar Kano, wanda Malam Abbas Ibrahim mataimakin sakataren ƙungiyar ƙwadago ta NLC, tsohon shugaban ƙungiyar ‘yan jaridu na ƙasa reshen Jihar Kano NUJ da ya wakilta a taron walimar da kuma ɗaurin auren Safiya Yakubu, da ya wakilci ƙungiyar ƙwadago a walimar da aka gabatar a ƙarshen makon da ya gabata a birnin Kano. Ya ce abin yaba wa NLC ne da sauran mahalarta taron.
Taron dai ya samu halarta da jawaban nasiha ga ma’aurata da fatan alkairi daga ‘yan jaridu manya da matasa a wannan walima kamar irin su Malam Aminu na kamfanin dillacin labarai ƙasar Faransa, Alhaji Ado Saleh Kankiya, Mustapha Muhammad, Malam Ali Kakaki, Malam Ibrahim Garba Daraktan yaɗa labarai na mataimakin gwamnan Kano da sauransu.

By ukarofi