An rutsa mahara a cikin kurkukun Jos

Daga BASHIR ISAH

A yammacin jiya Lahadi ‘yan bindiga suka kai hari gidan yarin garin Jos a Jihar Filato inda aka ce ‘yan bindigar sun maƙale a cikin gidan yarin sun rasa mafita sakamakon ƙawanyar da jami’an tsaro suka yi musu.

Mai magana da yawun hukumar kula da gidajen yari na ƙasa, CC Francis Enobore, shi ne ya bayyana haka a Abuja ran Lahadi da daddare.

Sanarwar da ta fito ta hannunsa ta ce, “Gungun ‘yan bindiga sun kai wa gidan gyaran hali na Jos, jihar Filato hari ɗauke da muggan makamai.

“An ce maharan sun dira gidan yarin ne da misalin ƙarfe biyar na yamma kuma ba tare da ɓata lokaci ba suka soma musayar wuta da masu gadin gidan yarin kafin daga bisani suka samu zarafin kutsawa ciki.

“Kodayake sun samu kutsawa cikin gidan yarin amma sun maƙale sun kasa fita sakamakon ƙawanyar da jami’an tsaro suka yi musu.

“Yanzu haka dai an samu cikakken kulawa da yanayin duba da alburusan maharan sun ƙare biyo bayan musayar wutar da suka yi da dakarun tsaron,” in ji Enobore

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *