Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Duk da fara aikin haƙo mai da wasu manyan matatun mai guda biyu suka yi a Nijeriya cikin watanni ukun da suka gabata, ‘yan kasuwar man sun ci gaba da shigo da man da kuma rarraba shi a faɗin ƙasar.
An tattaro a ranar Laraba cewa ‘yan kasuwa sun shigo da litar mai biliyan 2.3 na fetur tsakanin 11 ga Satumba zuwa 5 ga Disamba, 2024.
Ci gaba da shigo da man fetur ɗin ya saɓa wa sanarwar da wasu gungun ‘yan kasuwar suka yi a baya waɗanda tun farko suka bayyana aniyarsu ta dakatar da shigo da mai da kuma mai da hankali kan samun man a cikin gida.
Matatun man na cikin gida sun haɗa da matatun mai na Dangote mai ƙarfin tace gangan 650,000 a kowace rana da kuma matatar tace mai na Fatakwal mai ƙarfin tace 210,000 a jihar Ribas.
Matatar man Ɗangote ta fara sayar da man fetur ne a watan Satumba, yayin da matatar mai ta Area 5 ta fara aiki a ranar Talatar da ta gabata.
Duk da haka, binciken da jaridar The PUNCH ta yi a baya-bayan nan, ya nuna cewa a cikin kwanaki ukun da suka gabata, an shigo da jimillar man fetur tan 52,000 cikin ƙasar.
Kimanin litar nai 1322.76 ne ke yin tan. Wannan yana nuna cewa dillalai sun shigo da lita miliyan 68.74 na man cikin kwanaki uku.
