Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Fitaccen mawaƙin Hausa, Muhammad Birniwa, wanda aka fi sani da El-Mu’az, ya riga mu gidan gaskiya ne a ranar Laraba, 4 ga Disamba, 2024.
A cewar wata majiya mai tushe kamar yadda Mujallar Fim, mai bayar da labara a fagen finafinan Hausa, ta rawaito, marigayin ya halarci bikin abokinsa ne mawaƙi Auta Waziri ne ajali ya zo masa a lokacin da suke filin wasan ƙwallon ƙafa da ake yi na amarya da ango a filin wasa na Hamada Pitch da ke otel ɗin Hamdala akan titin Muhammadu Buhari a titin Waff Road.
A yayin da yake zaune sai aka ga ya miƙe yana faɗin jiri na ɗibar sa kuma nan take ya yanke jiki ya faɗi. Daga nan ne aka ɗauke shi zuwa wani asibiti mai suna Dialogue, inda a nan ne likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.
Kuma kafin faruwar al’amarin, marigayin ya shiga sahun matasan da suka buga ƙwallo a filin wasan, wanda ke nuna ƙoshin lafiyarsa, a cewar majiyar.
Marigayi El-Mu’az Birniwa, ɗan asalin ƙaramar Hukumar Birniwa ne ta Jihar Jigawa, sai dai haifaffen Kaduna ne, inda a nan ne ya girma kuma ya yi ɗaukacin rayuwarsa.
An dai yi jana’izarsa ne jiya Alhamis a Masallacin Zangon Daura na NDC a unguwar Kaji da ke Kaduna da misalin ƙarfe 1:00 na rana.
Kafin rasuwarsa, El-Mu’az ya rubata tare da rera waƙoƙi masu yawa kama daga na siyasa da soyayya da na faɗakarwa kan rayuwa ta yau da kullum. Kuma yakan shiga waƙar haɗaka, wato rubutawa da rera waƙa tare da wasu abokansa mawaƙa.
Wasu daga cikin waƙoƙin da ya rubuta ko ya rera tare da wasu mawaƙan sun haɗa da: Naka Sai Naka da Saƙon Murya ɗaya da ƙaunarki da Kafin Gaban Raini (wacce ya yi wa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i) da Haka Allah ya so (waƙar haɗaka tare da Yahaya Makaho) da Idan Ka Yarda (waƙar haɗaka tare da Ala da wasu) Ke Tawa Ce ( waƙar Auta Mg wanda ya sakaɗa El-Mu’az) da sauransu.
Wata hira da farfajiyar tattaunawa da jaruman Kannywood, Gabon Talk Room Show, wadda jaruma Hadiza Gabon ta yi hira da Marigayi El-Mu’az a shekarar da ta gabata, ya tabbatar da cewa shi ɗan jam’iyyar APC ne kuma sun mara wa tafiyar Buhari baya, haka ma tafiyar shugaban ƙasa na yanzu Bola Tinubu a yayin yaƙin neman zaɓen da aka yi na 2023.
Tuni dai mawaƙa da jarumai a masana’antar Kannywood suka fara miƙa saƙon ta’aziyyarsu inda Shugaban Kamfanin Fim na ƙasa, Ali Nuhu, ya wallafa ta’aziyyarsa da cewa, “Allah ya jiƙansa, Allah ya sa mutuwa hutu ce”.
Haka shi ma mawaƙi M. Shariff, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa.
Shi ma shahararen marubucin fim, Nazir Adam Salih, ya bayyana marigayin da cewa mutum ne mai fara’a, har ya kira shi da “gonar auduga” ga kuma iya mu’amala, “idan yau kuka haɗu da El-Mu’az a karo na farko zai karɓe ka kamar kun yi shekara guda, idan kuka sake haɗuwa da shi a karo na biyu, sai ka rantse da Allah tun kuna kuna yara tare kuka tashi da shi tare,” in ji Nazir.
Haka ma shahararren malamin Harshen Hausa a jami’ar Coglone da ke Jamus, kuma mai fashin baƙin kan finafinan Kannywood, Muhsin Ibrahim, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa inda ya nuna muhimmancin zama cikin shiri ga dukkan musulmi saboda mutuwa “ba ta sallama” idan lokaci ya yi da fatan Allah ya yi wa El-Mu’az gafara.
