An tabbatar da Alhaji Muhammad Barau a matsayin sabon Sarkin Kontagora

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Jihar Neja ta sanar da naɗin sabon Sarkin Sudan na Kontagora, kwanaki bayan rasuwar sarkin masarautar na shida, Alhaji Sa’idu Namaska.

Kwamishinan qananan hukumomi da ci gaban al’ummomi da masarautun gargajiya, Emmanuel Umar ne ya sanar da naɗin Mohammed Barau a matsayin sabon Sarkin Kontagoran, a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba da daddare.

Ya ce, an zaɓi sabon Sarkin Sudan na Kontagoran ne a ranar Lahadi 19 ga watan Satumban 2021, kuma manyan masu zavar sarki na masarautar ne suka yi hakan.

Kwamishinan ya ce “Masu zavar sarkin sun tabbatar wa Gwamnan jihar ta Neja, Muhammad Sani Bello cewa sun yi zaɓen ne ta hanyar bin dokokin al’adu na Masarautar Kontagora, kuma sun yanke hukuncin ne bisa fahimtar su ba tare da tsoma bakin wani daga waje ba.”

Sanarwar ta ce “a don haka kamar yadda doka ta tanadar wa gwamna, ya amince da matakin nasu tare da tabbatar da Mohammed Barau Kontagora a matsayin Sarkin Sudan na bakwai.