Sojoji sun bindige mahara uku a Inugu

Rundunar sojojin Nigeriya ta bayyana cewa, dakarun yanki na 5 na Atisayen GOLDEN DAWN da ke jihar Enugu sun bindige mahara uku bayan sun kai farmaki wurin bincike na ‘yan sanda kan hanyar Okija zuwa Onitsha ranar 7 ga Oktoban 2021.

Sanarwar manema labarai da rundunar ta fitar ta hannun Daraktan Hulɗa da Jama’a na Ƙasa na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ta nuna dakarun sun yi amfani da ƙarfin wuta wajen fin ƙarfin maharan a inda saura su ka tsere. ‘Yan bindigar uku waɗanda ke cikin motocin safa biyu ƙirar Hilux da Hummer sun kwanta dama, sauran kuma suka tsere.

Kazalika, rundunar ta ce dakarun sun cafke wata mota da babura biyu a yankin. Tare da cewa, “mun yi babban rashin soja ɗaya wanda ya sadaukar da ransa domin Najeriya.”

Babban hafsan sojojin Nijeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya, ya yaba wa dakarun bisa jajircewarsu. Ya kuma yi kira gare su da su ci gaba da kyakkyawan aikin su a yankin. Kana ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan sojan da ya kwanta dama yayin artabun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *