An yaba da ƙoƙarin Shugaban Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An yaba da irin ƙoƙarin Mataimakin Shugaban Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil, Farfesa Musa Tukur Yakasai, bisa jajircewarsa wajen bunƙasa jami’ar, lamarin da ya jawo hankalin Gwamnatin Tarayya har take kawo ayyukan tallafi da ci gaba ga jami’ar da ɗalibanta.

Shugaban ƙungiyar Nigeria Police Ambassadors (EXPOLS) reshen Jihar Kano, Ambasada Sulaiman Kabir, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da manema labarai.

Ya ce himma, ƙwazo da jajircewar Shugaban Jami’ar sun taka rawar gani wajen jawo hankalin Gwamnatin Tarayya ta amince da aiwatar da ayyukan da za su taimaka wajen haɓaka jami’ar.

A cewarsa, daga cikin ayyukan da aka amince da su akwai samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana (solar), wanda zai taimaka wajen inganta harkokin karatu da gudanarwa a makarantar.

Ambasada Sulaiman Kabir ya kuma yaba da gudunmawar Chancellor na jami’ar, Alhaji Aliko ɗangote, bisa ƙoƙarinsa na kawo ci gaba a fannoni daban-daban. Ya tunatar da alkawarin da ɗangote ya ɗauka a lokacin bikin yaye ɗalibai (Convocation) na bara, yana mai cewa tuni ya fara cika wannan alƙawari ta hanyar ɗaukar matakan da suka dace.

Haka kuma, ya jinjina wa Manajan Darakta na Hukumar Kula da Makamashi ta ƙasa, Dakta Mustapha Abdullahi, kan gudunmawar da ya bayar wajen aiwatar da ayyukan da aka amince da su a jami’ar.

Sulaiman Kabir ya jaddada cewa, babu shakka irin kishin aiki da jajircewar Farfesa Musa Tukur Yakasai sun haifar da gagarumin ci gaba a jami’ar, wanda ake gani a zahiri tun bayan hawansa kan muƙamin shugabanci.

Ya ƙara da cewa, irin wannan sadaukarwa da kishin ilimi ne ya sa Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ke yawan zaɓar Farfesa Yakasai domin wakiltarsa a muhimman taruka na jami’o’i daban-daban, sakamakon irin ƙwarewa da ficewar da yake da ita a harkar ilimi.

By ukarofi