Filato: Abin fashewa ya yi ajalin mutane biyu a gidan mai a Ɓokkos

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wani abin fashewa a wani gidan mai da ke Ƙaramar Hukumar Ɓokkos a Jihar Filato, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu a ranar Juma’a.

Haka kuma, mutane uku sun jikkata sakamakon faruwar al’amarin.

Mazauna yankin ciki har da Shugaban ƙungiyar masu sanya ido akan zaman lafiya, Kefas Mallai sun tabbatar da aukuwar iftila’in ga manema labarai a Jos, babban birnin jihar.

Mista Mallai ya ce, al’amarin ya faru ne a wani gidan mai da ke ƙauyen Daffo yayin da ake aikin kulawa na gyara wani tanki da aka binne a gidan man.

Ya ce, an samu aukuwar iftila’in ne a daidai lokacin da wani mai aikin walda da yaronsa suke gyara wani sashe na tankin.

A cewar Mallai, masu aikin sun fara gudanar da aikin nasu ne a lokacin da suka ga cewa babu komai acikin tankin, kuma ba su ga alamun wani haɗari ba da ka iya zama barazana ga rayuwarsu.

Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto, ba samu bayani na musamman ba daga hukumomi ba ko kuma sanin sunayen waɗanda iftila’in ya afka wa.

By Babaji