Kaduna: Matan APC sun jaddada goyon baya ga Uba Sani bayan baranta daga zanga-zanga

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar Wayar da Kan Matan Jam’iyyar APC ta Shiyyar Kaduna ta Tsakiya, ta bayyana cikakken goyon bayanta ga duk wani mataki da gwamnan jihar, Sanata Uba Sani zai ɗauka dangane da tsayar da ’yan takara a shiyyar, gabanin babban zaɓen 2027.

Ƙungiyar ta bayyana wannan matsaya ne yayin wani taro da ta gudanar a ɗakin taro na otel ɗin Hamdala da ke birnin Kaduna, inda ta jaddada cewa haɗin kai da biyayya ga shugabancin jam’iyya su ne ginshiƙin samun nasara a kowanne irin zabe.

Shugabar ƙungiyar, Vera Oladotun, ta bayyana cewa tana da yaƙini kan cewa matakan da gwamnan zai ɗauka za su taimaka wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar APC daga matakin ƙasa har zuwa jiha a zaben da ke tafe.

A wani ɓangare, ƙungiyar ta nesanta kanta daga duk wata zanga-zanga da wasu mata ke shirin gudanarwa a jihar Kaduna, inda aka danganta wannan yunƙuri da goyon bayan wani ɗan takara.

A cewarta, irin waɗannan matakai na iya haifar da rikici tare da haddasa rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar.

Kazalika, Oladotun ta jaddada cewa, ƙungiyar ba za ta shiga ko goyon bayan kowace irin zanga-zanga da sunan nuna rashin amincewa da wani ɗan takara ba.

“Mu a matsayinmu na mata masu kishin jam’iyya, mun ɗauki matakin nisanta kanmu daga duk wani abu da zai iya kawo sabani a cikin jam’iyyar.

Ta ƙara da cewa, “Muna kira ga daukacin matan APC da su ci gaba da mara wa gwamnatin Sanata Uba Sani baya domin ci gaban jihar da kuma tabbatar da nasarar jam’iyya a zabe mai zuwa.”

Har ila yau, Oladotun ta bayyana cewa idan har ƙungiyar za ta goyi bayan wani ɗan takara a matakin Majalisar Dattawa, to hankalinsu ya fi karkata ga Sanata Shehu Sani, wanda ta ce yana da kwarewa da gogewar wakiltar al’umma yadda ya kamata.

A cewarta, “Sanata Shehu Sani ya nuna jajircewa da sadaukarwa wajen kare muradun jama’a, kuma muna ganin ya cancanci sake wakiltar mu a Majalisar Dattawa.”

Ƙungiyar ta kuma yi kira ga sauran bangarorin jam’iyyar APC da su guji duk wani abu da zai haddasa rabuwar kai, tare da jaddada muhimmancin haɗin kai domin fuskantar ƙalubalen siyasa da ke gaba.

Mahalarta taron sun haɗa da shugabannin mata daga kananan hukumomi daban-daban na shiyyar Kaduna ta Tsakiya, inda suka bayyana aniyarsu ta ci gaba da wayar da kan mata kan muhimmancin shiga harkokin siyasa da kuma zabe.

A ƙarshe, ƙungiyar ta tabbatar da cewa za ta cigaba da shirye-shiryen fadakarwa da gangamin wayar da kai domin karfafa gwiwar mata su taka rawar gani wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a dukkan matakai a zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.

By Babaji